Ruwa ya yi barna a yankuna a Jigawa

Ambaliyar ruwa

Image caption

Ambaliyar ruwa na datse hanyoyi da janyo asarar dukiya

A jihar Jigawa ta Najeriya, mahukunta sun dukufa wajen kididdigar asarar da ambaliyar ruwa ta haddasa a wasu sassan jihar.

Al’amarin na zuwa sakamakon ruwan saman da aka shafe tsawon makwanni ana tafkawa. Garuruwan Sara, da Girambo sun samu kansu cikin tsaka mai wuya sakamakon datse hanyar da ruwan ya yi.

Ana amfani da keken Shanu dan ketarawa zuwa wasu garuruwa da kauyuka makusanta.

Garin Gantsa na cikin wuraren da masifar ta shafa a cikin kananan hukumomin jihar goma sha biyu, inda ta datse hanyoyin mota, ta kuma rusa gidaje tare da lalata amfanin goma.

Wani mazaunin garin Gantsa ya shaidawa BBC cewa da misalin karfe 12 na dare suka budi ido shi da iyalinsa a cikin ruwa, kuma ba su dauki dogon lokaci ba da ficewa daga gidan mai daki uku sai kawai ya rushe baki daya.

  • Guguwar Dorian: Mutun 5 sun mutu a Bahamas
  • Jihohi ’30’ ambaliyar ruwa za ta shafa a Najeriya

Ruwa ya cinye gari!

Dagacin Gantsa Alhaji Umar Mustapha ya ce bai taba ganin iftila’i irin hakan ba, komai da suka shuka na amfanin gona baki daya ruwan ya shafe.

Iyalan da lamarin ya shafa sun samu fakewa ne a makarantun da ke garin, sakamakon ba su da wurin zama.

Gwamnan jihar jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya ce kamar yadda waccan shekarar gwamnati ta taimakawa wadanda ambaliyar ta shafa musamman manona, wannan karon ma gwamnati ta aikewa gwamnatin tarayya dan ganin an taimakawa manoma da Iri da za su yi shuka a lokacin rani da nufin rage asarar da suka yi.

Ana yawan samun ambaliyar ruwa a wasu sassan arewacin Najeriya sakamakon ruwan saman da ake shekawa kamar da bakin kwarya.

A wasu lokutan kuma akan koka da cushewar magudanan ruwa na daga cikin matsalolin da ke kara haddasa ambaliyar ruwan a lokacin damina.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...