Rundunar sojin saman Nigeriya ta musa zargin cewa ta jefa bam wa masu Maulidi a Kaduna

Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta cewa tana da hannu a harin bam da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Wata majiya a Kaduna a wani rahoto da ta fitar ta yi zargin cewa jirgin da NAF ke aiki da shi ya bm da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi, lokacin da mutanen ƙauyen suka taru domin gudanar da bukukuwan Mauludi.

Lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Da take mayar da martani kan wannan ikirari, rundunar sojin saman ta bakin mai magana da yawunta, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana cewa NAF ba ta kai wani samame a Kaduna cikin awanni 24 da suka gabata ba.

Commodore Gabkwet ya ci gaba da tabbatar da cewa ba wai NAF kadai ce ke aiki da jiragen yaki marasa matuka a yankin ba.

More from this stream

Recomended