Rundunar Sojin Saman Najeriya Ta ce Ta Sami Gagarumar Nasara a Yakin Da Take Yi Da ‘Yan Ta’adda A Sokoto | VOA Hausa

A daidai lokacin da Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta sami gagarumar nasarori a yakin da take yi da ‘yan ta’adda a yankin gabashin jihar Sokoto, mazauna yankunan sun ce har yanzu ba za’a rasa fargaba ba, domin ‘yan bindigar suna nan kusa da jama’ar yankin.

Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air marshall Sadiq Baba Abubakar shi ne ya furta batun samun nasarar a wurin bikin da rundunar sojin sama da ke jihar Sokoton ta gudanar don taya murnar Sallah ga sojojin da ke bakin daga a yankin.

Air marshall Sadiq Baba Abubakar, ta bakin kwamandan rundunar dabarun kai farmaki da jirage, AVM Olusegun Philip ya ce, aikin da mayakan saman suke gudanar wa ya taikamaka gaya wajen dakile ayukan ta’addanci a yankunan.

Wasu daga cikin mazauna yankunan sun shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, sun gudanar da bikin sallah lafiya, ba tare da wani tashin hankali ba. Amma sun nuna damuwarsu da fargaba, domin a cewar su ‘yan bindigar suna kusa da yankunan nasu.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...