Rugar Fulani: Buhari ya yi Allah-wadai da kiran dattawan arewa | BBC Hausa

Fulani
Image caption

Kungiyar Fulani a Najeriya ta yi zargin ana siyasantar da duk batun da ya shafe su

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga Fulani makiyaya su yi watsi da kiran da kungiyar dattawan arewa ta yi musu na su baro Kudancin Najeriya domin komawa arewa.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar ta ce ”Dukkan ‘yan Najeriya suna da damar watayawa a kasar da zama a duk sassanta ba tare da la’akari da ainahin inda suka fito ba”.

Sannan “kundin tsarin mulki, da gwamnatin Najeriya za su bai wa dukkan ‘yan kasa kariya a duk inda suke,’ a cewar sanarwar wacce Garba Shehu ya sanya wa hannu.

A ranar Laraba ne kungiyar dattawan arewa ta (NEF), ta nemi Fulani da su bar Kudancin kasar domin komawa Arewa, abi da ake ganin martani ne kan adawar da shugabannin al’ummar yankin suka nuna ga shirin gwamnatin tarayya na samar da Rugagen Fulani a yankunansu.

Tuni dai jihohin arewa da dama suka yi maraba da shirin.

Batun samar da rugagen, wanda tuni aka dakatar, da kuma rikicin da aka dade ana samu tsakanin makiyaya da manoma, ke kara tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al’ummar kasar.

Ko a farkon makon nan sai dai tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya tashi tsaye domin shawo kan batun da sauran matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta a wata zazzafar wasika da ya aika masa.

  • Gaske ne an fara yarjejeniyar aure a Kano?
  • Afcon: A wane fanni kasashen da ke fafatawa suka yi zarra?
  • PSG ta ki karbar Coutinho da Rakitic a madadin NeymarSai dai sanarwar da fadar shugaban ta fitar, ta ce babu wanda ya isa ya bukaci wani ko wasu su yi kaura daga inda suke ko dai a arewaci, kudanci ko kuma yammacin Najeriya.

‘Gurbata tunanin makiyaya’Sanarwar ta ce kungiyar dattijan arewacin Najeriya ba ta da hurumin da za ta ce wasu su yi kaura daga inda suke zuwa ni sashe na kasar.

Sannan ta zargi kungiyar da wasu makamantanta da yin amfani da matsalolin tsaron da kasar ke fama da su wurin cimma bukatun siyasa.

”Don haka bai kamata a bari su ringa gurbata tunanin mutane musamman Fulani makiyaya ba,” a cewar Garba Shehu.

Ya kara da cewa gwamnati na iya bakin kokari domin ganin an magance matsalar da ke tsakanin Fulani makiyaya da manoma a sassa daban-daban na Najeriya ta hanyar maslaha don ganin dukkan bangarorin biyu sun yi na’am da hakan.

‘Ba kyamar Fulani muke yi ba’

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Rikici tsakanin makiyaya da manoma ya lakume rayukan dubban mutane a Najeriya

Shugaban kungiyar manoma ta All Farmers Asscociation of Nigeria (AFAN) reshen jihar Abia Cif Dunlop Okoro ya shaida wa BBC cewa “wannan shirin ba zai yi aiki a Najeriya ba.

Ya kara da cewa shirin ka iya zama mai kyau a wani wurin amma ba abu ne mai yiwuwa ba “musamman a Najeriya inda muke saurin zargin juna”.

“Yanzu mutane suna dari-dari da makiyaya sakamakon yawan samun rikici tsakaninsu da manoma. Saboda haka duk lokacin da ka yi maganar ruga babu wanda zai karbe ta.

“Ba ma kyamarsu domin kuwa ‘yan Arewa da suke zaune a kudu a yanzu sun fi wadanda suke zaune yawa kafin yakin basasar Biyafara. Haka su ma al’ummar Igbo da ke zaune a Arewa sun fi yawa a yanzu.”

‘Mun fi jin dadin yawo’

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akan yi wa Fulani lakabi da “Fulanin tashi” saboda yawon kiwo da suke yi

Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa wato al’ummar Fulani sun ce su fa sun fi son a bar su su ci gaba da yawo da shanunsu maimakon tsugunar da su da gwamnati ke shirin yi.

Ardo Sa’idu Baso shi ne sarkin Fulanin kudu maso gabas a Najeriya, ya ce ai in so samu ne a ce wata uku ko hudu shanunka su canza wurin zama.

Ya ce: “Mu a bar mu haka muna yawace-yawace da shanunmu ya fi mana a kan a tsugunar da mu a wuri daya. Inda shanu suka yi bazara ba nan suke shekara ba.

“Ya kamata a ce wata uku ko hudu shanu su canza wurin zama, mu mun fi jin dadin hakan.”

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...