Rubewar hakori: kun san yanda zaki ke kassara lafiyar hakoran yara?

Rashin kula na daga cikin abubuwan da suka sa yara a Afirka suka fi fama da ciwon hakori

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Likitocin hakori a Birtaniya sun bukaci gwamnatin kasar da ta sa makarantun kasar su daina bai wa yara cimaka mai zaki domin maganace rubewar hakora.

Sun ce hakan na da alfanu domin shawo kan matsalar wadda ke addabar kimanin kashi daya cikin hudu na yara ‘yan shekara biyar.

Haka nan masanan a harkar lafiya na bukatar ganin an kara sanya ido kan yadda yara ke wanke baki.

Kafin sauka daga mukami, Firaminista Theresa May ta sanar da wasu shirye-shirye na bunkasa lafiyar hakoran yara.

Sai dai sashin lafiyar hakori na kasar ya ce duk da an samu ci gaba a fannin, akwai bukatar a kara azama.

Wani kwararren likita a Najeriya Dakta Tanko Zakari, na asibitin koyarwa na Aminu Kano ya ce yara a yankin nahiyar Afirka sun fi na yankin Turai fama da wannan matsala ta rubewar hakori.

Ya ce, yawancin abubuwan da ke haddasa wannan matsala shi ne rashin ilimi da kuma hangen nesa game da lafiyar yara.

Sai dai ya ce matakin rage shan zaki, da kuma rungumar dabi’ar wanke baki za su iya hana rubewar hakora.

A cewarsa ‘ya kamata iyaye su tabbatar yara na wanke baki a kowane lokaci, a lokacin da za su tafi makaranta, da kuma lokacin da za su kwanta bacci.’

Shi dai bangaren kula da lafiyar hakorin na Birtaniya ya fitar da wani rahoto, inda ya bayar da shawarar daukan wasu matakai domin shawo kan matsalar rubewar hakori ga yara.

Shawarwarin sun hada da:

  • Dukkanin makarantu su fito da tsarin lura da yadda yara ke goge hakori.
  • Dukkanin makarantu su daina bai wa yara abinci mai sukari kafin shekarar 2022.
  • A takaita tallace-tallacen abinci masu dauke da sukari sosai.
  • A rage sukari da ake sanyawa cikin abincin jarirai da kamfanoni ke hadawa.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...