Rohr bai ce komai kan makomarsa a Super Eagles ba

Super Eagles

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Mai horas wa Gernot Rohr bai ce komai ba kan makomarsa a matsayin kocin Najeriya, bayan rade-radin lattin biyan albashi.

Mai shekara 66 dan kasar Jamus wanda yarjerjeniyarsa zai kare a Yunin 2022, bai karbar albashinsa a kan lokaci, tun da ya fara jan ragamar Super Eagles a watan Agustan 2016.

Hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF ta ce kocin na bin albashin watan Satumba ne kadaui, ba watanni uku ba kamar yadda rahotanni ke cewa.

Wasu rahotannin na cewar Rohr zai ja ragamar Super Eagles wasansa na karshe a wasan sada zumunta da Brazil a Singapore.

Tawagar kwakllon kafar Brazil da ta Najeria sun tashi 1-1 a wasan sada zumunta da suka yi, karo na biyu da suka fafata tun 2003, inda Brazil ta ci 3-0 a Abuja.

Tun kan nan Brazil ta buga 1-1 da Senegal ranar Alhamis 10 ga watan Oktoba a Singapore, a karawar ce Neymay ya buga wa Brazil wasa na 100.

Tsohon kocin tawagar Gabon da Niger da Burkina Faso ya kai Najeriya gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha, wanda Super Eagles ta kasa kai wa karawar zagaye na biyu.

Haka kuma Rohr ya kai gasar kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar, wanda Super Eagles ce ta yi ta uku a wasannin.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...