Rikicin Afghanistan: Taliban ta fara neman ma’aikatan tsohuwar gwamnati

Masu suka na ganin ya yi wuri a amince da ikirarin Taliban na cewa ta sauya kan yadda a ka santa a shekarun 1990.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Mayakan Taliban

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Kabul na Afghanistan na cewa mayaƙan Taliban sun shiga farautar yan ƙasar da suka shafe tsawon shekaru suna yi wa abokan gabarsu aiki.

Wata sanarwar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an samu labarin cewa mayaƙan sun fara bi gida-gida suna neman waɗanda suka yi wa gwamnatin da ta shuɗe da kuma kungiyar tsaro ta NATO aiki.

Idan har hakan ta tabbata, wannan mataki ya yi hannun riga da iƙirarin ƙungiyar na yin afuwa ga abokan gaba.

Masu suka na ganin ya yi wuri a amince da iƙirarin Taliban na cewa ta sauya kan yadda aka santa a shekarun 1990.

Jami’in Majalisar ĆŠinkin Duniya da ya jagorancin rahoton Christian Nellemann, ya faÉ—a wa BBC cewa “Taliban ta tsara bin sawun mutane da dama a Ć™asar da ta ke zargi an haÉ—a kai dasu wurin murĆ™ushe Ć™ungiyar.

”Kuma akwai yiyuwar hukunta iyalansu a madadinsu idan ba su miĆ™a kansu ba”, in ji Nellemann.

Ya ƙara da cewa dama ƙungiyar Taliban na da sunayen waɗanda take nema, kuma akwai fargabar zartar da hukuncin kisa kan mutane da dama.

A gefe guda, an gudanar da zanga-zangar ƙin jinin ƙungiyar a garuruwa da dama da suka haɗa da babban birnin ƙasar wato Kabul.

Wasu rahotanni sun ce an samu asarar rayukan fararen hula yayin irin wannan bore a birnin Asadabad.

A wata mai kama da haka an gano cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu bayan faɗowa daga jirgin Amurka Zaki Anwari ne, wani matashin ɗan ƙwallon kafa na Afghanistan.

Kasashen duniya da dama na ci gaba da kwashe yan ƙasarsu daga Afghanistan.

Kawo yanzu Amurka ta ce ta kwashe mutun 7,000, duk da rintsin da a ke ci gaba da fuskanta a filin jirgin saman Kabul.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa a yanzu Taliban ce ke da iko da dubban tankokin yaƙi, da jiragen yaƙi 30 zuwa 40 haɗi da tarin ƙananan makamai.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Taliban ta ƙwace iko da birnin Kabul da sauran yankunan ƙasar, bayan da shugaban ƙasa da sojojin ƙasar waje da sauran dakarun Afghanistan suka fice.

Nasarar da Taliban ta yi ya maido da ƙungiyar kan madafun iko bayan murkushe ta da Amurka ta yi tsawon shekaru 20.

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce tunda Taliban ta bayyana cewa tana son ƙulla hulɗar diflomasiyya da kuma samun karɓuwa ga ƙasashen duniya, ya rage gareta ta yi abinda ya dace.

(BBC Hausa)

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...