Rikici tsakanin ‘yan Najeriya da Kenya a kan Lupita

Lupita

Hakkin mallakar hoto
AFP

Fada ya kaure tsakanin ‘yan Najeriya da takakwarorinsu na kasar Kenya a shafin twitter saboda zabar wata jaruma ‘yar kasar Kenya, Lupita Nyong’o ta fito a matsayin ‘yar Najeriya a wani shirin fim.

Fim din mai suna Americanah, labari ne na wata mata ‘yar Najeriya da ta je karatun jami’a a Amurka da kuma dawowarta Legas.

An samo labarin dake fim din Americanah ne daga wani littafi wallafar Chimamanda Ngozie Adichie, wanda ya yi fice har ya samu babbar kyauta a 2013.

Tun bayan sanarwar da kamfanin shirya fina-finai na WarnerMedia ta fitar a makon jiya, ‘yan Najeriya ke ta nuna adawarsu a shafin twitter, cewa bai dace a zabi Nyong’o ‘yar kasar Kenya, wacce ta taba lashe kyautar jarumar fim na Oscar ba, ta fito a matsayin ‘yar Najeriya a fim din.

A cewarsu, zai fi dacewa a sanya ‘yar Najeriya da za ta iya magana da harshen ‘yan Najeriya ta fito a matsayin ‘yar kasar.

“Fitowar Lupita a matsayin zai fuskanci matsala daya… magana da harshen Ibo,” a cewar wani a twitter.

Wannan kuma na cewa: “Akwai kyawawan jarumai mata ‘yan Najeriya da za su fi iya yin abun da ake bukata.”

A nasu bangaren, ‘yan Kenya a shafin twitter sun yi ta kare zabin da aka yi wa Nyong’o, inda suke wa ‘yan Najeriya shagube da cewa ai ba Nyong’o ce ta “kawo rashin aikin yi a Najeriya ba” saboda ta zama kwararriyar jaruma.

Wasu kuma sun tunatar da ‘yan Najeriyar cewa ba a sanya dan yankin gabashin Afirka ko daya ba a wakar BeyoncĂ© da aka sanya fim din ‘The Lion King’ wanda kamfanin Disney ya sabunta, duk da cewa an yi amfani da yanayin kurmin kasar Kenya wajen tsara fim din.

[ad_2]

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...