Raunin Ansu Fati ya sake dawo masa

Ansu Fati

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona za ta buga gasar La Liga ranar Laraba a gidan Rayo Vallecano ba tare da Ansu Fati ba.

Dan wasan ya ji rauni a karawar El Clasico da Real Madrid ta doke Barcelona da ci 2-1 ranar Lahadi a Camp Nou.

Barcelona ce ta sanar da cewar dan kwallon mai shekara 18 na jin radadi a raunin da ya yi.

”Ansu Fati na jin radadi a kafarsa ta hagu. Ba zai buga wasa da Rayo Vallecao ba, samun saukinsa ne zai tabbar da ranar da zai dawo tamaula.” Kamar yadda ta sanar a Twitter.

Bayan da Ansu Fati ba zai buga karawar Laraba ba, kungiyar na sa ran Memphis Depay da Philippe Coutinho da kuma Sergio Aguero za su taka mata rawar gani.

Barcelona mai kwantan wasa tana ta tara a kan teburin La Liga nab ana.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...