
Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta bayar da umarnin gaggawa na rufe makarantar haɗaka ta gwamnatin ta tarayya da ake kira da FGC Kwali kan barazanar tsaro.
A wata sanarwa ranar Litinin jami’in yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar,Ben Goong ya alakanta daukar matakin da matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu daga cikin garuruwan dake kusa da makarantar.
Ya ce ministan ilimi,Adamu Adamu shi ne ya bayar da wannan umarnin a safiyar ranar Litinin kuma za a kara karfafa matakan tsaro a dukkanin makarantun haɗaka dake fadin kasar nan.