‘Rashin haihuwar maza na da alaka da kansar mafitsara’

Dad and baby

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa maza masu matsalar rashin haihuwa na da yiwuwar kamuwa da kansar mafitsara.

Wannan binciken da aka wallafa a wata mujallar kiwon lafiya ya yi dubi ga mata masu ciki miliyan daya da dubu dari 2 a kasar Sweden na tsawon shekaru 20.

Mazan da suke amfana da hanyar ICSI – wacce hanyar dashe ce da ake yin allurar maniyin namiji a tsakiyar kwan mace – suna da yiwuwar kamuwa da kansar mafitsara.

Amma masu bincike kan kansar mafitsara a Birtaniya sun bayyana cewa ya kamata a duba abubuwa da suka hada da yawan shekaru kafin a bayyana cewa maza masu larurar rashin haihuwar sun fi yiwuwar kamuwa da kansar mafitsara.

Masu bincike daga jami’ar Lund da ke Sweden sun bayyana cewa sun yi amfani da bayanai daga matattarar ajiye bayanan haihuwa da rajisatar jama’a.

Sun yi duba ne kan haihuwar da aka yi daga shekarun 1994 zuwa 2014 inda kuma suka duba wadanda suka samu larurar kansar mafitsara.

Akasarin jariran wato kashi 97 cikin 100 an samu cikinsu ne ta hanyar jima’i, sai kuma kashi 1.7 cikin 100 aka samar da su ta hanyar dashen maniyi a mahaifa, duk da bayanan basu nuna cewa rashin haihuwar maza ko matan ne ya janyo aka yi dashen ba.

An haifi jarirai 14,882 wato kashi 1.3 cikin 100 kenan ta hanyar ICSI.

An fara amfani da hanyar ICSI ne a shekarar 1992 a Sweden, inda duk lokacin da aka yi amfani da wannan hanyar ana rubutawa a rajista domin tarihi

‘Yin gwaji’

Cikin rukunin wadanda aka samu cikinsu ta hanyar jima’i, 3,244 wato kashi 0.28 cikin 100 an samesu da cutar kansar mafitsara idan aka hada da guda 77 wato kashi 0.37 cikin 100 a rukunin wadanda aka yi dashen maniyi ta hanyar IVF da kuma guda 63 wato kashi 0.42 cikin 100 na wadanda aka yi masu dashen maniyi ta hanyar ICSI.

Mazan da ke cikin rukunin ICSI su ma na cikin wadanda ke da yiwuwar kamuwa da cutar kansa ta mafitsara kafin su kai shekara 55.

Farfesa Yvonne Lundberg Giwercman wacce ta jagoranci binciken ta shaida wa BBC cewa: ”Yawan masu cutar mafitsara ba yawa, amma wadannan mazan duka masu kuriciya ne.”

”Rukunin mazan matasa ne da suke cikin barazana kuma ya kamata mu sa ido a kansu.”

Ta bayyana cewa tana sa rai cewa nan gaba za a kara bincike domin ganin alakar da ke tsakanin mazan da kuma kamuwa da cutar.

”Karancin hujjoji’

Amma Simon Grieveson daga kungiyar bayar da agaji ta masu fama da kansar mafitsara ta Birtaniya ya bayyana cewa yana da kyau kada a yanke hukunci sakamakon wannan bincike.

”Ana yawan samun kansar mafitsara musamman a maza wadanda suke sama da shekaru 50. Mazan da aka yi wannan binciken a kansu basu kai wadannan shekarun ba, kuma ba su da yiwuwar kamuwa da cutar.”

”Wannan binciken yana da kyau ya duba rukunin shekaru daban-daban domin fahimtar ko mazan da ke shan magani domin larurar rashin haihuwa na da yiwuwar kamuwa da cutar.”

”Idan za a iya tabbatar da hakan, ana bukatar kara zurfafa bincike domin gano musabbabin matsalar. Har sai an yi hakan, za a iya cewa babu wata kwakkwarar hujja da za a iya cewa za a karu idan an sa ido kan wadannan mazan.”

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...