Rashin aiki ya zama bala’i na kasa | BBC Hausa

wasta mata a Afirka ta Kudu na shanya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Fatara da rashin aikin yi sun fi wanzuwa a tsakanin bakar fata a kasar ta Afirka ta Kudu

Jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu ta ce arzikin cikin gida na kasa ya ragu da kashi 3.2 cikin dari a wata ukun farko na wannan shekara idan aka kwatanta da shekaru uku na karshen shekarar da ta gabata.

Babban Sakataren jam’iyyar, Ace Magashule ya ce wannan shi ne koma-baya mafi muni a cikin shekara goma, a kasar ta Afirka ta Kudu.

Sakatare Janar din yana bayani ne a wani taron manema labarai a wurin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar a karshen mako.

Shi dai wannan taro, zama ne da yake hado kan ‘yan kwamitin zartarwa na jam’iyyar ANC hadi da ‘yan kungiyoyin da ta yi hadaka da su na kwadago tare kuma da ‘yan majalisar dokokin kasar nata.

Sakatare Janar din na ANC, ya gaya wa manema labaran a hedikwatar jam’iyyar a birnin Johannesburg cewa, ‘sun kaddamar da matsalar rashin aikin yi a matsayin bala’i na kasa.

Sannan ya ce jam’iyyar mai mulki za ta bunkasa tattalin arzikin kasar ta yadda zai amfani dukkanin ‘yan Afirka ta Kudu da kuma samar da ayyukan yi.

Wannan dai shi ne taro irinsa na farko tun bayan da jam’iyyar ta yi nasara a babban zaben kasar a watan da ya gabata, inda ta samu kashi 57 cikin dari na kuri’u.

Jami’in ya ce wani karin dalili na yin wannan taron shi ne domin nazari a kan dumokuradiyyar kasar ta shekara 25 da kuma tsara yadda za su aiwatar da manufofinsu na neman samar da tartibin shiri na shekara biyar, don ciyar da kasar gaba.

Jam’iyyar ta ANC ta duba nasarar da ta yi tun lokacin da ta hau mulki a shekara ta 1994, inda ta ce tattalin arzikin kasar ya burunkasa bayan gomman shekaru na koma-baya a karkashin mulkin tsiraru farar fata.

Sannan ta ce arzikin kasar ya linka har sau uku kuma aikin yi ya linka biyu a tsawon wannan lokaci na mulkin da take yi tun bayan karbe ragamar iko daga mulkin wariyar launin fata.

Jam’iyyar wadda ta taso da fafutukar ‘yanto bakar fatar kasar tsawon shekara 107, ta ce, duk da wannan ci-gaba wanzuwar fatara da rashin aikin yi da rashin daidaito musamman a dalilai na wariyar launin fata da bambanci tsakanin maza da mata sun ci gaba da kasancewa.

Sai dai ANC din ba ta ambaci illar cin hanci da rashawa ba da aka samu a kasar ta Afirka ta Kudu, karkashin mulkinta.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...