Ranar Talata za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a Turai

Cristiano Ronaldo and Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Cristiano Ronaldo ya amince da komawa Manchester United, ko Kylian Mbappe zai koma Real Madrid a bana?

Kungiyiyon Premier League sun kashe kusan fam biliyan daya, kuma daf a rufe kasuwar saye da sayen ‘yan kwallo a Ingila a bana.

Ranar Talata ake sa ran Manchester United za ta kammala daukar Cristiano Ronaldo daga Juventus.

Tun farko an dauka kyaftin din tawagar Portugal, zai koma taka leda a Manchester City ne, amma sai ya zabi komawa United, bayan shekara 12 da barin kungiyar.

A cinikin da aka yi a bana, tuni Ole Gunnar Solskjaer ya sayo Jadon Sancho kan fam miliyan 73 daga Borussia Dortmund da dan kwallon tawagar Faransa, Raphael Varane daga Real Madrid kan fam miliyan 34.

Asalin hoton, Getty Images

Mai rike da kofin Premier League, City ta kafa tarihin daukar dan wasa mafi tsada a Birtaniya, shine da ta sayo Jack Grealish daga Aston Villa kan fam miliyan 100.

Kawo yanzu kungiyoyin Premier League sun kasha fam miliyan 962 wajen sayo ‘yan wasan tamaula a bana, bayan da a bara aka kasha fam biliyan 1.3.

Mai rike da kofin Champions League, Chelsea ita ce ta biyu wajen sayen dan kwallo da tsada, bayan da ta sake daukar Romelu Lukaku daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Cinikin ‘yan wasa shida da aka yi mafi tsada a Birtaniya, Lukaku ya kafa tarihi daga biyu a ciki

Arsenal ta kashe fam miliyan 140 wajen kara karfin kungiyar, wadda ta dauki ‘yan wasa da yawa ciki har da fam miliyan 50 da ta biya Brighton aka ba ta Ben White, da Martin Odegaard da ta sayo daga Real Madrid kan fam miliyan 30 da kuma mai tsaron raga Aaron Ramsdale daga Sheffield United kan fam miliyan 24.

Haka kuma Gunners ta soke kwantiragin Willian ta kuma samu rarar fam 200,000 da take biyan sa albashi a kowanne mako, dan Brazil din zai koma Corinthians da taka leda.

Ita kuwa Liverpool ta dauko mai tsaron baya, Ibrahima Konate daga RB Leipzig kan fam miliyan 36.

Aston Villa kuwa ta yi amfani da wasu kudin da ta sayar da Grealish, inda ta dauki Danny Ings da Emiliano Buendia da kuma Leon Bailey.

Asalin hoton, Getty Images

Ba za a manta da kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta Turai ta bana ba, bayan da Paris St Germain ta dauki Lionel Messi daga Barcelona.

PSG ba ta tsaya iya nan ba, domin tun farko ta dauki mai tsaron ragar Italiya, Gianluigi Donnarumma da Ashraf Hakimi da Sergio Ramos da kuma Georginio Wijnaldum.

Yaushe za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a bana?

Za a rufe kasuwar cinikayya a Premier League da English Football League da kuma a Scotland ranar Talata 31 ga watan Agusta da karfe 23:00 na dare agogon Birtaniya.

Ranar Alhamis za a fara buga wasannin neman gurbin shuga gasar cin kofin duniya, watakila wasu ‘yan kwallon ba za su saka hannu kan yarjejeniya ba sai bayan mako mai zuwa.

Yaushe za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa a Turai?

‘Yawancin kasashen Turai za su kammala hada-hada ranar Talata da tsakar dare.

Za a rufe kasuwar Jamus da karfe 17:00, yayin da za a karkare cinikayya a Sifaniya da Italiya da kuma Faransa ranar Talata da misalin karfe sha biyun dare agogon Birtaniya.

Ko za a yi hada-hada da yawa a ranar karshe?

Dan kwallon Tottenham, Harry Kane ya ce zai ci gaba da wasa a kungiyar zuwa karshen kakar bana.

Tun farko an yi hasashen cewar zai koma Manchester City da taka leda, daga baya kyaftin din Ingila ya sanar zai yi zaman sa a Tottenham.

A bara ‘yan wasa 12 aka dauka a ranar karshe a Premier League – hakan bai kai yawan hada-hadar da aka yi a kasuwannin baya ba.

Sai dai watakila a samu motsawa a Chelsea ko dai ta sayo ko kuma ta sayar, ana cewa kungiyar ta Stamford na son sayo Jules Kounde daga Sevilla kan fam miliyan 68.

Wasu rahotannin na cewar Borussia na son daukar Callum Hudson-Odoi.

Watakila Real Madrid ta hakura da sayen Kyalian Mbappe daga Paris St Germain duk da tayin da ta gabatar, bayan da kungiyar Faransa ta ki sallama tayin mata.

Ana alakanta West Ham da cewar tana son mallakar dan kwallon Manchester United, Jesse Lingard, wanda ya taka rawar gani a wasannin aro da ya buga mata a bara.

Ita kuwa Leicester City tana tattaunawa da RB Leipzig kan daukar Ademola Lookman, yayin da Wolves ke son ganin ta mallaki dan kwallon Lille, Sven Botman.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...