Pep Guardiola zai ci gaba da jan ragamar Man City zuwa 2023

Pep Guardiola

Pep Guardiola ya sa hannu kan yarjejeniyar shekara biyu, domin ci gaba da horar da Manchester City zuwa karshen kakar 2023.

Mai shekara 49 ya lashe kofin Premier League biyu da FA Cup da League Cup uku, tun lokacin da ya koma kungiyar a 2016.

Tun farko kwantiragin tsohon kocin Barcelona da Bayern Munich zai kare ne a karshen kakar tamaula ta bana.

Shekara biyar da Guardiola ya yi a City, ita ce kungiyar da ya dade yana jan ragama tun bayan da ya zama kocin tamaula a 2008.

Idan Guardiola ya kammala yarjejeniyarsa a kungiyar zai zama na biyu da ya dade a Manchester City, matakin da Joe Mercer ke kai a yanzu.

Wanda yake na daya da ya dade yana horar da City shi ne Les McDowall, wanda ya ja ragamar wasa 592 tsakanin 1950 da kuma 1963.

Kawo yanzu da Guardiola ke aikin horar da City, kungiyar ta yi nasara a wasa 181 daga 245 da ta fafata, wato ya yi nasara kaso 73.87 cikin 100 kenan.

(BBC Hausa)

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...