PDP, SDP sun yi watsi da sakamakon zaben Kogi tun kafin a kammala hada sakamako | BBC Hausa

Uche Secondus

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Shugaban jam’iyyar PDP na Najeriya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya ta gargadi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC da kada ta amince da sakamakon zaben gwamna da aka kawo mata, musamman na karamar hukumar Okene da ke jihar Kogi.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa an rubuta sakamakon ne kawai da kai, ta yadda zai bai wa jam’iyyar APC mai mulkin jihar nasara, inda ta bukaci da a gaggauta soke sakamakon.

A wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa Kola Ologbondiyan, jam’iyyar ta ce sakamakon da aka bayyana a rumfunan kada kuri’a ne kawai ya kamata hukumar zaben ta yi amfani da shi, ba wanda aka kawo mata a cibiyar tattara sakamako da ke garin Lokoja ba.

Ita kuma jam’iyyar SDP a wata sanarwa ta hannun ‘yar takarar gwamna a karkashin jam’iyyar Natasha H. Akpoti, ta ce ba a yi zabe ba a daukacin yankin Kogi ta tsakiya.

  • Kai-tsaye: Sakamakon zaben Kogi a Najeriya
  • Bai wa jihar Kogi kudi a yanzu rashin gaskiya ne – PDP

Sanarwar ta ce “A ‘yan kalilan din wurare da aka nuna kamar an yi zabe, an yi amfani ne da takardar kada kuri’a ta shekarar 2015, inda aka rinka rubuta jam’iyyar SDP da fensir a jikin takardar kada kuri’a.”

SDP ta yi zargin an yi amfani da ‘yan bangar siyasa wajen tarwatsa masu zabe da kuma hana su fitowa kada kuri’a.

Da safiyar ranar Lahadi ne dai hukumar zaben ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.

Ya zuwa tsakar ranar Lahadin, gwamna mai ci Yahaya Bello na jam’iyyar APC shi ne ke kan gaba a yawan kuri’u a sakamakon da INEC ta bayyana.

Yayin da dan takara na jam’iyyar PDP Musa Wada ki biye masa.

Ko a ranar Asabar din da aka yi zaben cibiyar tabbatar da ci gaban demokradiyya a Najeriya CDD, wadda ta sanya ido a zaben ta yi zargin an yi magudi ta hanyar satar akwatunan zabe da kuma sayen kuri’a.

More News

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...

Delta: An dawo da gawarwakin sojojin da aka kashe Abuja don yi musu jana’iza

Gawarwakin sojojin da aka kashe a jihar Delta kwanan nan sun isa maƙabartar sojoji ta kasa da ke Abuja. Gawarwakin sun iso ne da misalin...