PDP na so Peter Obi ya dawo jam’iyar – Damagum

Shugaban riƙo na jam’iyar PDP,Umar  Damagum ya ce jam’iyar bata fara ƙoƙarin haɗewa da wasu jam’iyyu  ba.

Damagum ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin “Nigeria Right Now” na gidan talabijin din AIT.

Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam’iyar LP ya ziyarci Atiku Abubakar mutumin da ya yiwa jam’iyar PDP ta karar shugaban ƙasa a 2023 da kuma wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyar.

Da aka tambaye shi kan ziyarar Damagum ya kaucewa tambayar inda ya bada amsa cikin wayo.

Ya ce Obi bai ziyarce shi ba kuma shi ba mutum ba ne mai shige-shige da zai sa sai ya ji abun da ganawar ta Obi ta mayar da hankali akai.

Da aka tambaye shi ko ko yana son Obi ya dawo PDP shugaban na PDP ya ce ” Ba wai Obi kaɗai ba kowane mutum da ya taba kasancewa dan jam’iyar PDP muna son ya dawo.”

More from this stream

Recomended