Osimhen ya koma Galatasaray da wasa

Ɗan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen ya isa ƙasar Turkiyya inda zai fara buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray dake  ƙasar.

Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan saukarsa a filin jirgin sama na Istanbul ya nuna murnarsa matuƙa kan irin tarbar da ya samu.

Dubban magoya bayan ƙungiyar ɗauke da ganguna  ne suka tarbe shi.

Ɗan wasan mai shekaru 25 ya koma ƙungiyar ne a matsayin aro daga ƙungiyar Napoli da yake buga wasansa acan bayan da dangantaka tayi tsami a tsakaninsu.

Ƙungiyar ta Æ™asar Turkiyya za ta dauki nauyin biyan albashin Osimhen a tsawon lokacin aron  amma kuma babu tilashin sai sun saye shi a Æ™arshen kakar wasannni.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka Æ´anbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...