Obama ya gargadi ‘yan jam’iyyar Democrat kan zaben 2020 | BBC Hausa

Former US President Barack Obama speaks to guests at the Obama Foundation Summit

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barack Obama ya ce “Babu Ba’amurken da ke son ganin an rusa tsarin rayuwarmu baki daya domin yin gyara.”

Toshon shugaban Amurka Barack Obama ya gargadi ‘yan jam’iyyarsa ta Democrat masu neman tsayawa takarar mukamin shugaban kasa, ya nemi su yi hattara kan rungumar tsare-tsaren da a zahiri ba masu yiwuwa ba ne.

Mista Obama ya ce ‘yan Democrat na iya raba gari da masu zabe idan suka ci gaba da karkata bangaren masu ra’ayin rikau a siyasance.

Tsohon shugaban na magana ne yayin wani taron tara kudade domin zaben shekara ta 2020, kuma ya ce yawancin masu zabe ba sa son ganin, “an rusa tsarin rayuwarmu baki daya domin yin gyara.”

Kawo yanzu Mista Obama bai bayyana dan takarar da yake mara wa baya ba.

A halin yanzu akwai ‘yan takara 18 da ke neman zama wanda jam’iyyar ta Democrat za ta tsayar a matsayin dan takarar da zai kalubalanci Shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasa na 2020.

Wadanda ke kan gaba a halin yanzu su ne tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da Sanata Elizabeth Warren da Sanata Bernie Sanders da kuma Pete Buttigieg, wanda shi ne magajin garin South Bend na jihar Indiana.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barack Obama tare da tsohon mataimakinsa Joe Biden a 2008, lokacin suna kan mulki

Wane ne zai kara da Trump a 2020?

Saura kasa da shekara guda a gudanar da zaben shugaban Amurka, kuma ‘yan jam’iyyar Democrat na ta kokarin fitar da dan takarar da zai ja daga da shi.

Alkaluma na baya-bayan nan na nuna Joe Biden da Elizabeth Warren da Bernie sanders da kuma Pete Buttigieg ne ke kan gaba cikin masu neman mukamin su 18.

More News

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...