NYSC: Matasa na muhawara kan soke tsarin hidimar ƙasa

One youth corper

Asalin hoton, Twitter/@nysc_ng

Ƙudirin doka da zai hana yin hidimar ƙasa a Najeriya ya wuce mataki na biyu a zauren Majalisar Wakilan Najeriya.

Honarabul Awaji-Inombek Abiante mai wakiltar yankin Opobo/Nkoro ne ya miƙa ƙudirin da ke da burin soke shirin na NYSC, kamar yadda ya ce saboda matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.

Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce a shafin sada zumunta na Twitter a ƙasar musamman a tsakanin matasa inda wasu ke ganin soke shirin mataki ne mai kyau yayin da wasu kuma ke ganin bai dace a soke ba.

Hidimar ƙasa ta NYSC na buƙatar duk ɗan Najeriyar da ya kammala makarantar gaba da sakandire da shekarunsa ba su haura 30 ba ya yi wa ƙasar hidima ayankin ƙasar da ba nan ya fito ba.

Misali, ƴan kudu a kan tura su arewacin ƙasar su ma ƴan arewa a kan tura su kudancin ƙasar.

Amma kafin nan sai an yi masu atisaye mai kama da na sojoji kafin tura su gudanar da ayyuka a makarantu ko asibitoci ko bankuna da dai sauran hukumomi.

Sai dai kawo yanzu, matsalar tsaro na nema ta zama barazana ga wannan tsarin musaman yadda sace-sacen mutane ya yi ƙamari a Najeriyar.

Wannan mai amfani da shafin na Twitter mai suna Mohnice ta ce a ganinta hidimar ƙasa ɓata lokaci ne don haka tana goyon bayan soke shi.

Ta ce tsarin ba shi da amfani saboda ɗaliban da suka yi karatu a Burtaniya suna da tabbacin samun aiki suna kammala karatu, waɗanda suka yi karatu a Najeriya ba su da tabbas din samun aikin ko bayan kammala hidimar kasar.

Shi ma wannan mai suna Aliyu Dahiru Bello ya bayyana cewa NYSC ba ya ƙara wa Najeriya da masu hidimar ƙasar komai.

Ya ce tsarin ya zamar wa gwamnati wani nauyi kuma yana jefa masu hidimar kasar cikin haɗari, ya ce yana goyon bayan soke tsarin.

Shi kuwa wannan mai amfani da shafin Emperor Segun ya ce ba ya ganin akwai alfanu a soke tsarin NYSC.

Ya bayyana cewa a lokacin da ya yi hidimar ƙasa a jihar Edo, kashi 95 cikin 100 na malaman makarantar da ya koyar masu hidimar ƙasa ne. Ya ce haka ma a asibitin unguwar da ya yi aiki.

Moses Olalowo mai amfani da Twitter ya ce soke tsarin NYSC zai shafi kowa har da gwamnati.

Ya ce hukumomin gwamnati da masu zaman kansu sun dogara ne da ƴan hidimar ƙasa musamman tunda ba a biyansu albashi mai tsoka.

“Ƴan hidimar ƙasa sun ne fatan wasu al’ummomi don samun ingantaccen ilimi,” a cewarsa.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miƙata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaƙi da yiwa tattalin arzikin ƙasa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...