Nukiliya: Faransa da Iran sun tattauna

Shugaban Iran Rouhani daga hannun dama yana duba nukiliya a farko shekarar nan.

Hakkin mallakar hoto
AFP

–BBC Hausa

Image caption

Shugaban Iran Rouhani daga hannun dama yana duba nukiliya a farko shekarar nan.

Shugaban Iran Emmanuel Macron ya tattauna da takwaransa na Iran Hassan Rouhani ta wayar tarho inda ya nuna damuwarsa kan matsalar da Iran din za ta iya fuskanta idan ta ci gaba da saba yarjejeniyar da aka yi a 2015 kan shirin Nukiliyar Iran din.

Shugabannin biyu sun bayyana cewa a mako mai zuwa za su yi kokarin duba sharuddan yarjejeniyar domin sabunta tattaunawar da aka yi kan yarjejeniyar.

Iran din ta ce a ranar Lahadi za ta yi bayani kan irin ci gaban da take samu wajen kara inganta sinadarin Uranium dinta wanda hakan zai kara saba ka’idojin da aka gindaya na yarjejeniyar nukiliya.

Iran din dai na bukatar kasashen Turai da su nemi hanyoyin da za su bi domin rage tasirin takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran din da suka shafi tattalin arzikin kasar.

Sanarwar da ta fito daga Faransar ta bayyana cewa Mista Macron zai ci gaba da tuntubar bangaren Iran din da sauran abokan hulda na kasashen waje domin rage fargabar da ke akwai a kasa.

Yarjejeniyar shirin nukiliyar na Iran na ci-gaba da zagwanyewa, in ban da dan abin da ya rage kalilan wanda ya hana ta wargajewa baki daya, a yi baran-baran.

A bana dai ana ta samun sabani tsakanin Amurka da Iran tun bayan da Amurka ta zargi Iran da kai wa jiragen dakon mai biyu hari a mashigar tekun Oman.

Bayan nan kuma Iran din ta harbo jirgin yakin Amurka a mashigar Tekun Hormuz, abin da Trump ya kira ”gagarumin kuskure” wanda yake ganin Iran din ta yi.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...