Najeriya ta yi shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola | BBC Hausa

Medical staff on the Ugandan border

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Ma’aikatan lafiyan da aka tura kan iyakar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Uganda a bakin aiki

Najeriya ta ce ta bullo da matakai don shirin ko-ta-kwana kan cutar Ebola wadda ke kara bazuwa tun bayan barkewarta a Jamhuriyar Dimokradiyya Kongo da kuma Angola a baya-bayan nan.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta ce kwamitin shirin tunkarar cutar ebola a Najeriya ya dauki matakai da dama ciki har da tabbatar da ganin cibiyar kai daukin gaggawa ta kasa na aiki kuma a yanzu haka tana cikin shirin ta-kwana.

Haka zalika, ayarin jami’an kai daukin farko na kasa suna nan a cikin shirin kai agaji cikin sa’a 24, idan bukatar haka ta taso.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta ce matakan sun zo ne sakamakon aikin tantance hatsarin bazuwar cutar ebola daga kasashen Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Uganda zuwa Najeriya, wadda aka tabbatar kasadar ‘yar kadan ce.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta ce tana bibiyar bullar kwayar cutar ebola a kasashen biyu.

A ranar 11 ga wannan wata ne ma’aikatar lafiyar Uganda ta tabbatar da bullar cutar ebola a lardin Kasese kusa da kan iyakar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

An gano cutar ce a jikin wani yaro dan shekara biyar bayan wata ziyara da ya kai yankin Mabalako a jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo inda ya halarci jana’izar kakansa, wanda cutar ta yi ajalinsa a ranar 1 ga watan Yuni.

Hukumomi sun gano tare da tantance mutum takwas da yaron ya yi hulda da su kuma tuni aka fara bibiyarsu kut-da-kut.

Cibiyar takaita yaduwar cutuka a Najeriya ta ce jami’an lafiya a jihohin da ke manyan hanyoyin shigowa irinsu Lagos da Kano da Abuja da Fatakwal suna cikin shirin ta-kwana.

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...