Najeriya ta rufe ofishin kungiyar Action Aid kan Boko Haram | BBC Hausa

Aid bags

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Rundunar sojin Najeriya ta dakatar da ayyukan kungiyar agaji ta kasa da kasa, Action Aid mai yaki da talauci bisa zargin kungiyar da hannu wajen samar wa Boko Haram abinci da magunguna.

Rundunar ta ce ta gargadi kungiyar agajin kan agazawa Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Action Against wacce ta musanta zarge-zargen, ta ce taimakon take samar wa mutanen da rikici ya shafa na fuskantar kalubale.

Rikicin kungiyar ‘yan-tada-kayar-bayan da aka shafe shekara 10 ana yi ya halaka mutane sama da 30,000.

Fiye da mutum miliyan biyu kuma sun rasa matsugunansu.

Wata gamayyar kungiyoyin farar hula na taimakawa gwamnati wajen agazawa mutanen da aka tilastawa barin gidajensu.

A shekarar 2018, rundunar sojin kasar ta taba zargi hukumar kula da kananan yara ta MDD, UNICEF da zama ‘yar leken asirin masu tada-kayar-baya, abin da ya sa ta haramta kungiyar wacce a nata bangaren ta musanta zarge-zargen.

Sai dai daga baya, gwamnatin ta janye haramcin.

Cikin wata sanarwa, Action Aid ta ce tana samar da taimako ne ba tare da wata manufa ta daban ba ga miliyoyin mutane a jihar Borno ta hanyar samar masu da kayayyakin agaji ga mutanen da rikici ya fi shafa musamman mata da yara kanana.

Kungiyar ta ce sojoji, ba tare da wata sanarwa ba, sun bukaci ta rufe ofishinta da ke birnin Maiduguri a jihar Borno.

Cikin watan Yuli, Action Aid wacce ke da mazauni a Paris ta ce ma’aikatan ta masu ba da ceto sun shiga hannun masu garkuwa a Najeriya.

An ga ma’aikatan shida cikin wani bidiyo, inda daya daga cikinsu take kira ga gwamnatin kasar da al’ummar kasar waje da su sa baki a kubutar da su.

Kawo yanzu, babu wanda ya san inda ma’aikatan suke.

Babu kuma wata kungiya da ta fito ta ce ita ce ta sace ma’aikatan.

A shekarar 2015, Boko Haram ta kwace iko da kaso mai tsoka na Borno abin da ya ba ta damar fadada ayyukanta zuwa makwabtan kasashe.

Yakin kawo karshen masu tada-kayar-baya da sojoji suka kaddamar ya sa gwamnati kwato mafi yawan yankunan da suka fada hannun Boko Haram.

Sai dai a baya bayannan, masu tada tarzomar sun fadada kai harin kunar bakin wake da sace-sacen jama’a domin cimma muradunsu.

Daya daga cikin hare-hare mafi muni da ta kai shi ne kan makarantar ‘yan mata ta Chibok da ke arewa maso gabashin kasar lokacin da aka yi garkuwa da dalibai ‘yan mata 276.

Da yawa daga cikinsu sun kubuta, amma dai har yanzu ba a kai ga gano inda wasu 100 suke ba.

Rahotanni na cewa tun daga 2013, Boko Haram ta sace mutane fiye da 1,000.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...