
Hukumar NAFDAC dake tabbatar da ingancin magunguna da abinci a Najeriya ta ce taliyar Indomie da ake a Najeriya bata da illa ga lafiyar jikin dan adam.
Hukumar ta ce taliyar ba ta ɗauke da sinadarin Ethylene oxide.
Jami’an lafiya ne a ƙasashen Malaysia da kuma Taiwan su ka ce sun gano sinadarin ethylene oxide a cikin Indomie mai ɗauke da sinadarin ɗanɗanon kaza.
Ethylene oxide wani nau’in sinadari ne da bashi da wari ko kuma kala da ake amfani da shi wajen kare kayayyakin kiwon lafiya daga dauka ko kuma kawar da cututtuka da kayan
Shugabar hukumar ta NAFDAC, Mojisola Adeyoye ta ce Hukumar ta gudanar da gwajin kan nau’o’in taliyar daban-daban daga cikin samfuran da suka ɗauka a kasuwanni da kuma kamfanonin yin taliyar dake faɗin ƙasar nan.
An gudanar da binciken kan samfura 114 na taliyar tare da sinadarin ɗanɗanon dake cikin su.