‘Na shafe fiye da shekara 50 ina yi wa shugabannin Nijar dinki’ | BBC Hausa

Keken dinki

Hakkin mallakar hoto
Singer India

Wani tela da BBC ta tattauna da shi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ya ce ya shafe sama da shekaru 50 ya na dinki, kuma daga cikin wadanda ya ke yi wa dinkunan har da shugabannin kasar.

Telan mai suna Alhadji Abubakar Sulaiman wanda ake kira Abba Tchiroma, ya ce tun daga kan shugaban kasa zuwa ministoci da ma sauran mutanen gari, ba wanda ba ya yi wa dinki.

Ya ce daga cikin shugabannin da ya yi wa dinkin, ba wanda ya fi yi wa dinki kamar Tandja Mamadou, sai kuma Mamman Usman da dai sauransu.

Abba Tchiroma, ya ce shugaban kasar daya ne kawai bai yi wa dinki ba wato Mahammadou Issoufou.

Telan ya ce ba wani abu ba ne ya sa ya samu nasara a wannan sana’a ta sa ba illa cika alkawari.

Ya ce ‘ Cika alkawarina na ne ya sa manyan mutane ke kawo mini dinki, domin idan aka kawo mini dinki na ce ga lokacin da za a zo a karba, to bana saba alkawari’.

Telan ya ce wasu manyan mutanen labarinsa ma suke ji a kan cika alkawarin, shi ya sa ma suke garzayawa suna kawo masa dinkin.

Abba Tchiroma, ya ce ‘ A tsawon shekarun da na shafe ina dinki, bana jin akwai wanda na taba sabawa alkawari gaskiya’.

Bayani a kan Halayyar teloli

A mafi akasarin lokuta teloli kan saba alkawari, wannan kuwa wata halayyace da aka sansu da ita.

Wannan dalili ne ya sa mutane kan canja teloli akai-akai saboda rashin cika alkawarinsu.

Da wuya kaga wani ko wata ta rike tela guda, dole sai ka ga mutum guda na da teloli daga biyu zuwa sama.

A irin wannan halayya ta teloli ta rashin cika alkawari, a wasu lokuta har rigima kan kaure tsakanin tela da kwastoma, wani lokacin sai an kai ga hukuma wato ‘yan sanda.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...