Na hannun daman Shugaba Buhari Isma’ila Funtua ya rasu

@BashirAhmaad

Bayanan hoto,
Alhaji Isma’ila Isa Funtua mashahurin mai harkar kafafen yada labarai ne a Najeriya kuma makusanci ga Shugaba Buhari

Allah Ya yi wa wani makusancin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Mallam Isma’ila Isa Funtua rasuwa.

Ya rasu ne sakamakon bugun zuciya ranar Litinin, a cewar ɗaya daga cikin ‘yan uwansa.

“Mallam ya faɗawa iyalinsa cewa yana son ganin likita amma sai da ya fara zuwa wajen mai aski. Daga nan kuma ya tuƙa mota zuwa asibiti,” in ji ɗan uwansa wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa.

An rawaito cewa za a yi jana’izar marigayin ranar Talata. Isma’ila Isa ɗan kasuwa ne kuma jami’in gwamnati da ke da ƙwarewa ta sama da shekara 30.

Marigayin ne ya assasa kamfanin Bulet International, babban kamfanin ƙere-ƙere da ya gina mahimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya.

Alhaji Isma’ila Funtua ne kuma daraktan gudanarwa na farko na jaridar Dimokrat sannan ya taɓa zama shugaban ƙungiyar NPAN na kusan shekara takwas.

More from this stream

Recomended