Mutumin da ya kashe mata 93 a Amurka | BBC Hausa

Matan da Samuel Little ya kashe

Hakkin mallakar hoto
FBI

Image caption

FBI ta fitar da zanen hotunan matan da Samuel Little ya ce ya kashe da nufin gano ainihin mutanen.

Hukumar bincike ta Amurka FBI ta tabbatar da cewa mutumin da aka tsare bayan ya yi ikirarin kashe mutane 93 a tsawon shekara 40, shi ne ya fi aikata laifukan kisa a tarihin kasar.

‘Yan sanda sun alakanta Samuel Little mai shekara 79 da 50 daga cikin laifukan kisan kai da aka aikata daga 1970-2005.

Tun a 2012 aka yanke wa Samuel Little hukuncin daurin rai da rai saboda kisan wasu mata uku.

Hukumomin kasar sun ce mutane masu rauni ne Little ya fi kai wa hari, yawancinsu mata bakar fata ne, wadanda akasarinsu masu zaman kansu ne da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Little wanda tsohon dan damben boksin ne, kan naushi mutanen ne su fadi kafin ya makure su. Hakan na nufin ba kowa ne lokaci ake ganin alamun da ke nuna kisan gilla aka yi wa mutanen ba.

Sakamakon haka, hukumar FBI ta ce ba ta binciki sauran kisan kan ba, sannan ta yi kuskuren ayyana hadari ko shan kwaya fiye da kima a matsayin musabbabin mutuwar wasu daga cikin mutanen.

”Kwararrunmu sun yi amannar cewa “Dukkan bayanan da ya yi abin dogaro ne”, a cewar hukumar, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.

“A tsawon shekaru Samuel Little ya dauka asirinsa ba zai tonu ba, saboda yana ganin ba wanda ke lissafa mutanen da ya kashe,” in ji Christie Palazzolo, kwararriyar mai binciken manyan laifukka ta FBI.

Sanarwar ta kara da cewa: “Ko da yake an riga an daure Little a gidan kaso, FBI na ganin dacewar a bi wa kowa ce rai da ya kashe hakkinta – domin a kammala binciken yadda ya kamata.”

Jami’an tsaro na cigaba da bincike domin tantance sauran kisan kai 43 da Samuel Little ya yi ikirarin aikatawa.

Hakkin mallakar hoto
Wise County Jail

Image caption

Hoton da hukumomi suka dauki Samuel Little wanda rahotanni ke cewa yana kuma amsa sunan Samuel McDowell

Jami’an hukumar sun fitar wa jama’a karin bayani a kan wasu kisan kai biyar da aka aikata a Kentucky da Florida da Louisiana da Nevada da kuma Arkansas a kokarinsu na gano mutanen da ba a tabbatar da mutuwar tasu ba.

A baya FBI ta fitar wa jama’a hotunan da Little ya zana a gidan yari, kuma ya ce na mutanen da ya kashe ne, a kokarin hukumar na gano karin wasu mutanen da ya kashe.

Sun kuma fitar da hotunan bidiyon hirar da aka yi da Little inda a ciki yake siffanta kisan kan.

A daya daga cikin laifukan kisan kai biyar da FBI ke neman taimakon jama’a domin kammalawa, Little ya kwatanta yadda ya hadu da wata mata bakar fata mai suna Marianne ko Mary Ann a Miami a jihar Florida, a shekarun 1970.

Little ya kuma siffanta wa jami’an yadda ya kashe matar mai shekara 19 a kan wata hanya da ke kusa da wata gonar rake, sannan ya ja gawarta ya kai cikin jeji.

“Kasar na da taushi,” in ji Little. “Da na juya ta sai ta fadi a ruf da ciki.”

A wani karon kuma, Little ya siffanta yadda ya makure wata mata a 1993 a dakin otal a Las Vegas. Ya ce kafin lokacin ya taba haduwa da dan matar har suka gaisa. Ya ce bayan kashe matar sai ya je wajen gari ya jefar da gawarta a wani kwari.

Image caption

Taswirar da ke nuna mutanen da ake zargin Little ya kashe, daga rumbun bayanan FBI

Jami’ai sun ce yawancin kwatancen da Little ya bayar daidai ne, amma rashin tuna ainahin ranakun da abubuwan suka faru na kawo cikas a binciken.

Babu tabbacin ko akwai karin laifukan da za a tuhumi Little da su sakamakon bayanansa na baya-bayan nan.

A 2012 aka tsare Little bisa zargin ta’ammali da kwaya a Kentucky, sannan aka mika shi zuwa California, inda jami’an tsaro suka gudanar da bincike kan kwayar halittarsa ta DNA.

Kafin nan Little ya taba aikata miyagun laifuka da suka hada da fyade da fashi da makami a sassan Amurka.

Daga nan aka tura shi zuwa shirin tsare masu aikata miyagun laifuka (ViCAP) – shirin da ke nazari kan masu yawan aikata muggan laifuka da fyade. Shirin na mika wa hukumomin tsaro na cikin gida bayanan da ya tattara domin duba alakarsu da wasu laifukan da ba a riga an shawo kansu ba.

A bara, wani jami’in kula da gandun daji a jihar Texas James Holland tare da wata tawagar ViCAP sun je California inda suka yi wa Litte tambayoyi.

Jami’an sun ce Little ya amince ya yi magana da su ne saboda yana so ya girgiza gidajen yari. Holland ya samu damar yi wa Little tambayoyi “kusan kullum,” sannan ya samu cikakkiyar fahimtar laifukan Little yadda ya kamata.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...