Mutanen Anaca sun yi takaicin sace yara Kanawa da aka yi | VOA news

Yanzu haka, ra’ayoyi na ci gaba da bayyana kan batun yara guda 9 da aka sace daga sassan birnin Kano, aka kuma sayar da su a garin Anaca jihar Anambra, inda jama’a da dama suka yi Allah wadai da lamarin suka kuma bukaci mahukunta da su dauki kwakkwaran mataki akan wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

Mista John Eze ya ce, “Irin wannan abin bai dace ba, kuma abu ne mai muni sosai. Bai kamata a rangwanta ma duk wanda ya aikata irin wannan laifin ba. Sannan ya ce, akwai hadin bakin wasu mazaunan unguwannin da aka sato yaran, saboda bai yiwuwa a sace yaran ba tare da hada baki da wasu ‘yan unguwa ba. Kuma akan batun canza musu addini da suna da aka yi, ya ce ya na ganin matsafa ne suka juya musu kwakwalwa, yadda zai kasance duk abin da aka gaya musu, sai su yi. Ya kamata hukuma ta hukunta duk wanda ya aikata irin wannan laifin. Kuma banda wannan, ya kamata a ci gaba da gudanar da bincike, don kubutar da sauran yaran da irin wannan al’amarin ya shafa.”

Malama Chinonyerem Ndubuisi, ta ce “Irin wannan abin bai da kyau. Kuma da yake ‘yan kabilar Igbo ne aka kama, lallai akwai Hausawan da aka hada baki dasu aka sace yaran nan. Tunda an gano irin wadannan mutanen, ya kamata a hukuntasu sosai don na baya su hankalta.”

Shi ma Anselm Nkemka, ya ce, “Kafin a samu irin wannan kuskure, dole ne da hannun na gida a ciki, mai sayar da yara daga Kano. Kuma wannan mutune za a kokarta a gano ko su waye da kuma mabuyarsu. Idan aka kama su, to ka san an warware wannan matsalar. Saboda haka, kamata ‘yan sanda su kara gudanar da bincike a Kano, don har yanzu akwai abubuwan da basu bayyana ba.”

A yayin da Mista Onyebueke Ike ya karkare batun da cewa: “Wannan abun bai dace ba. Ya yi matukar muni. Kuma tunda an riga an kama wadannan bata-garin, ya kamata a hukuntasu daidai da laifin da suka aikata. Ya ce yana kira ga iyaye da su kara jan damara wajen kula da ‘ya’yansu. Kowa ya kara mayar da hankali kan yaransa.”

A ranar Juma’ar da ta wuce ne rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane shida (6) bisa zargin garkuwa da wasu yara guda tara (9), da kuma sayar dasu a garin Onitsha, inda masu saya suka canza musu addini.

More News

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...