Mutane biyu sun mutu wasu da dama sun jikkata a ruftawar gini a Abuja

Mutane da dama ne aka samu nasarar cetowa daga cikin baraguzan wani ginin bene da ya ruguzo a birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne Layin Lagos dake kauyen Garki a Garki dake Abuja da tsakar daren ranar Laraba.

A cewar wata majiya dake wurin da lamarin ya faru akalla mutane 37 aka samu nasarar cetowa daga cikin baraguzan ginin inda aka kai su asibiti domin samun kulawa.

Kawo yanzu dai mutane biyu aka tabbatar da sun mutu a lamarin.

Hukumomin birnin dai basu fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin amma hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da Nyesom Wike ya kama aiki a matsayin sabon ministan Abuja inda ya ci alwashin kawo sauye sauye da dama a birnin.

More from this stream

Recomended