Mutane biyar sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a jihar Niger

Wani ƙazamin rikici a tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Beji dake ƙaramar Bosso ta jihar Niger ya jawo asarar rayukan mutane biyar ciki har da mutane uku ƴan gida ɗaya.

Rikicin ya samo asali ne a ranar Litinin bayan da aka gano gawar wani manomi a gonarsa kwana guda bayan da yayi ƙorafin cewa shanun wasu makiyaya sun shiga gonarsa sun cinye masa shuka.

A cewar mazauna garin gano gawar manomin ce a ranar Talata ya haifar da É“arkewar rikicin tare da jefa garin da kewayensa a cikin zullumi musamman ma saboda a ranar Laraba kasuwar garin take shirin ci.

Aliyu Muhammad mazaunin garin ya ce lamarin ya jefa  fargaba da tsoro a zukatan al’umma.

Ya ce irin haka ce ta faru a watan Nuwamban shekarar 2023 mutane shida suka rasa rayukansu ranar kasuwar garin sanadiyar rikici.

Wani bafulatani ya ce ƴan bijilante sun tare titin Minna zuwa Zungeru inda suka riƙa zaƙulo Fulani matafiya daga cikin motocin abun ya ƙara saka damuwa a zukatan mutane.

More News

Jam’iyar PDP ta dakatar da Dino Melaye

Jam'iyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Dino Melaye tsohon ɗantakarar gwamna a jihar kan zargin cin amanar jam'iya. Shugabannin jam'iyar PDP na mazaɓar...

Sojoji sun kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Buzu

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun samu nasarar kashe gawurtaccen É—an bindiga Kachalla Halilu Sububu wanda aka fi sani da Kachalla Buzu. An kashe Kachalla ne...

Dakarun Najeriya sun hallaka Æ´anbindiga a Neja

Rundunar sojin saman Najeriya ta hakala 'yanbindiga sama da 28 a yankin ƙaramar hukumar Shiroro dake jihar Neja.Wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai...

Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai. Wannan ce ganawa...