Muna Duba Yiwuwar Tilasta Baiwa Mata Sojoji Damar Sanya Hijabi -Majalisa

Majalisar wakilan Najeriya na ci gaba da tattaunawa a kan wannan kuduri da ke neman bai wa sojoji mata da takwarorinsu da ke aiki da hukumomin tsaro a kasar damar sanya hijabi idan suna bukata.

A cikin kudurin, Sashe na 13 na neman a hana rundunar soji da dukkan wasu kungiyoyin tsaro masu zaman kansu a Najeriya musgunawa duk wata jami’a da ta zabi sanya hijabi a bakin aiki.

Sashe na 13 karamin sashi na 2 na wannan kuduri, ya bukaci rundunar soji a Najeriya ta samar da kariya ta musamman ga duk wani jami’i da ya zaÉ“i gudanar da al’amuransa dai dai da tsari da manufa, da kuma koyarwar adinin da yake bi.

Amma kuma kudurin bai tanadi wani hukunci da za’a iya yankewa duk wanda ya saba shi ba, ko da yake ya bayyana yin hakan a matsayin aikata laifi da za’a iya hukunta mutum a kai.

Dan majalisar wakilai daga mazabar Bida da Gbako da Katcha a jihar Naija Saidu Abdullahi ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar, inda ya ce yayi haka ne don ganin yadda sanya hijabin ke neman zama wani abin muhawara a Najeriya duk da dokar kasa ta bayar da damar sanyawa.

Dan majalisar ya kara da cewa, wannan kuduri ya kuma nemi a ba da kariya ga dukkan masu bin addinai ba akan maganar hijabi ba ce kadai a cikin kudurin ba.

Ya ce “mun san cewa ba Musulmai ne kadai ke fama da matsalar nuna musu wariya ba, har da Kiristoci ma suna fama da wannan matsala, wasunsu ma ba sa iya yin magana.”

Haka kuma dan majalisar ya ce, “a wasu lokutan, akwai wurin da kila Kirista zai iya samun kan sa a inda Musulmai ke da rinjaye kuma shi ma ya gamu da irin wannan matsala, saboda haka wannan kuduri zai sama masa kariya.”

A halin yanzu dai kudurin ya tsallake karatu na biyu, kuma majalisar wakilan za ta ci gaba da tattaunawa kafin a kai ga amincewa da shi idan hali ya yi, a cewar Saidu Abdullahi.

Batun sanya hijabi a makarantun wasu sassan Najeriya dai na ci gaba da jawo cece-kuce musamman a kwanakin baya-bayan nan nan a jihar Kwara, inda har ta kai ga rufe makarantu da haddasa tashin hankali tsakanin mabiya addinin musulunci da kuma na kirista.

Tuni dai, yan Najeriya da dama ke ta tofa albarkacin bakin su kan kudurin a kafaffen sada zumunta, inda wasu ke marhaba da shi wasu kuma ke yi watsi da kudurin tare da cewa, akwai abubuwa masu mahimmanci kamar tsaro da ya kamaÅŸa yan majalisar su mayar da hankali a kai.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...