
Asalin hoton, H@HQNIGERIANARMY
Majalisar wakilan Najeriya ta ce ta tashi tsaye don kawo ƙarshen al’adar shiga aikin soja don neman abinci maimakon kishi da cancanta da son bautawa ƙasa, abin da ga alama ke janyo zubewar darajar aikin.
Ta ce dole ne a lalubo hanyoyin magance matsalar nuna tsoro da ragwantaka a cikin aikin ta yadda za a ƙarfafa kwarewa da jajircewa cikin rundunonin sojin ƙasar.
“Shi ya sa daga sun je bakin daga, an ji ƙarar bindiga, sai a zura da gudu. Ka ga wannan abin ya kamata a nemi magani kansa,” in ji mai tsawatarwa na majalisar wakilai Mohammad Tahir Monguno.
Ya kuma ce suna so a yi gyara ta yadda za a daina ɗaukar mutane aikin soja a ƙasar, saboda shi ɗan wani ne, ko kuma ƙanin matar wani babba ne da zai nema masa alfarmar shiga aikin.
Ɗan majalisar na wannan jawabi game da binciken da suke yi kan batun murabus ɗin wasu ɗaruruwan sojoji cikin ‘yan kwanakin nan a Najeriya.
An sha ba da rahotanni a Najeriya kan yadda sojoji a wasu lokutan suke tserewa daga fagen daga yayin artabu da ‘yan ta-da-ƙayar-baya a yankin arewa maso gabas.
Majalisa ta kuma lura da yadda manyan mutane a ƙasar ciki har da ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati na cusa ‘ya’yansu cikin aikin tun daga kwalejin horas da manyan sojoji ta NDA, cewar Monguno.
Ya ce kamata ya yi duk wani ɗan Najeriya ya iya shiga aikin soja matuƙar ya cancanta kuma yana da ƙwarewa da gudunmawar da zai bayar wajen gina ƙasa.
“Muna so wannan ma a gyara, ta yadda kowa zai iya shiga aikin soja bisa cancanta ba tare da nuna alfarma ko fifita wani ba”.
Da aka tambayi Monguno ko wacce hujja suka dogara da ita ta yin waɗannan kalamai. Sai ɗan majalisar ya ce: “Ai mu ‘yan Najeriya ne.”
Asalin hoton, @HQNIGERIANARMY
Mu ‘yan Najeriya ne, duk abin da yake faruwa a ƙasa, za mu sani. Kuma mu, muna cikin mutane, mu ‘yan majalisa ne, muna wakiltar mutane. Duk abin da mutane suke faɗa muna sani, in ji shi.
Ya ce majalisar wakilai ta bai wa kwamitinta mai kula da harkokin sojin ƙasa da ke bincike kan murabus ɗin sojojin Najeriya 356 tsawon mako guda don ya gabatar da rahotonsa.
Kuma a tsawon wannan lokaci, ana sa rai kwamitin zai gana da sojojin da suka sanar da yin murabus da kuma su kansu manyan hafsoshin sojin Najeriya har ma da ministan tsaron ƙasar.
Monguno ya ce jazaman ne binciken ya tattaro shaida kan dalilan da ke janyo irin wannan yin murabus na ɗumbin sojojin Najeriya tashi ɗaya.
Shin lokacin murabus ɗin su ne ya yi bisa doka? Ko kuwa akwai waɗansu dalilai da suka sanya su barin aiki? Ɗan majalisar ya tambaya.