‘Mun ceto ‘yan makaranta shida daga hannun masu garkuwa’

Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta ceto dalibai guda shida da masu garkuwa suka sace da safiyar Alhamis , a jihar Kaduna.

Sojojin sun ce masu garkuwar dai sun sace ‘yan matan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa makaranta.

Rundunar sojin ta ce baya ga ‘yan matan an kuma yi garkuwa da wasu ‘yan tasi guda uku, inda sojojin da ke kusa da inda abin ya faru suka bazama neman wadanda aka yi garkuwar da su bayan samun labari.

Sojojin sun ce sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan musayar wuta da masu garkuwar inda har wani daga cikin masu satar mutanen da samu rauni, sannan kuma sauran ‘yan bindigar suka arce.

  • An sace shugaban makaranta a Kaduna
  • Tsoron garkuwa na sa jama’a jure wuya a tashar jirgin kasa

Wannan ne dai karo na uku da ake sace ‘yan makaranta a cikin mako guda a jihar ta Kaduna.

A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne dai aka sace ‘yan mata guda 6 da malamansu guda biyu daga makarantar sakandare ta kwana ta Engravers College. Kuma har yanzu ba wani labari. A ranar Alhamis din nan kuma aka sace shugaban wata makarantar fasaha a jihar ta Kaduna.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...