Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya makon da ya gabata

Kamar kowane mako, mukan tattaro muku wasu abubuwan da suka faru a ƙarshen mako, a wannan makon ma, mun tattaro muku muhimman abubuwan da suka faru daga 13 ga watan Satumba zuwa 19 ga watan Satumba.

El-Rufai ya rattaɓa hannu kan dokar yi wa masu fyade dandaƙa

A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya rattaɓa hannu kan dokar hukunci mai tsanani a kan duk wanda aka kama da laifin fyade.

Dokar ta ba da damar kisa ko yin dandaÆ™a ga duk wanda aka kama ya yi wa Æ™ananan yara ‘yan Æ™asa da shekara 14 fyade.

Haka ma ƙarkashin dokar, za a iya yanke musu hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

Idan a ka kama mace kuwa dokar ta ce za a cire mata bututun ɗaukar ƙwai zuwa mahaifa ko kuma a kashe ta.

Ƴan bindiga sun kai wa Æ´an sanda hari a Sokoto ‘sun kashe DPO’

A makon da ya gabata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari a garin Gidan Madi da ke ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Maharan sun kai harin ne a ofishin Æ´an sanda a tsakar dare kuma har sun kashe DPO a garin, kamar yadda wasu mazauna garin suka shaida wa BBC.

Wani mazaunin garin ya ce suna bacci suka ji ƙarar harbe-harben bindiga, wanda ya tayar da su daga bacci.

Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar wa BBC da harin, amma kakakin ƴan sandan jihar, ASP Muhammad Sadiq bai yi ƙarin haske ba musamman game da kashe DPO da ƴan bindigar suka yi ba.

Baya ga kashe DPO, mazauna garin sun kuma ce Æ´an bindigar sun yi awon gaba da wasu mata a garin na Gidan Madi.

Buhari ya amince da sauya fasalin aikin ‘yan sanda a Najeriya

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaÉ“a hannu a dokar kawo sauye-sauye ga aikin ‘yan sanda a Æ™asar.

Dokar ta tanadi yadda rundunar ‘yan sandan za ta kasance mai Æ™arin nagarta da kuma kyakkyawan tsari a aikinta, bisa manufofi na tabbatar da gaskiya da rikon amana a tafiyar da lamuranta da albarkatunta.

Dokar kuma ta tanadi wani tsari na musamman da rundunar za ta rinÆ™a samun tallafin kuÉ—i kamar yadda wasu manyan cibiyoyin gwamnati suke samu, haka kuma za a Æ™ara inganta aikin ta hanyar horo na musamman da za a rinÆ™a ba jami’an.

Aikin ‘yan sanda a Najeriya na daga cikin ayyukan da suka yi Æ™aurin suna ta fannin cin hanci da rashawa, kuma ana zargin hakan ya samo asali ne sakamakon rashin kyakkyawan tsari da aka É—ora aikin tun a farko.

Gwamnatin Buhari ta bai wa ƴan Najeriya haƙuri kan kuskuren bayanin cike sabon fom na banki

A makon da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta nemi afuwar Æ´an kasar kan wani sabon fom É—in banki da ta fitar kuma ta bukaci su shiga bankunansu su cike.

Gwamnatin ta ce akwai kura-kurai a kan bayanin da tsarin cike fom din don haka ta goge sakon da ta wallafa na neman bukatar cike wannan fom din.

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriyar ta wallafa sanarwar a shafinta na Tuwita inda ta buƙaci ƴan ƙasar da su shiga bankunansu su cike wani sabon fom.

Sannan masu amfani da banki fiye da É—aya dole sai sun shiga bankunan sun cike sabon fom É—in. Tsarin kuma ya shafi duk wani mai asusu a banki da suka haÉ—a da kamfanonin.

More News

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ÆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...