Mene ne tarihin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto?

Bukola Saraki da Tambuwal

Hakkin mallakar hoto
Tambuwal’s Twitter

Kotun koli a Najeriya ta tabbatar wa Aminu Waziri Tambuwal na PDP kujerarsa ta gwamna ranar Litinin bayan ta yi watsi da karar da Ahmed Aliyu na APC a jihar Sokoto ya shigar gabanta.

Tambuwal ya yi nasara a zaben Sokoton da kuri’u 512,002, bayan da ya doke abokin hamayyarsa, Ahmed Aliyu da ya samu kuri’u 511,660.

Shi dai Ahmed Aliyu ya kalubalanci nasarar Tambuwal a gaban kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar sai dai kotun ta yi watsi da kokensa.

Wannan dalili ne ya sa Ahmed ya kara daukaka kara zuwa Kotun Koli domin kalubalantar Tambuwal.

Sai dai hukuncin kotun na yanzu na nufin Ahmad Aliyu na APC ba zai iya sake kai kara ko ina ba, sai dai ya hakura.

Menene tarihin Tambuwal?

An haifi Aminu Waziri Tambuwal ranar 10 ga watan Janairun 1966 a kauyen Tambuwal da ke jihar Sokoto.

Ya shiga makarantar Firamare a 1979 sannan ya shiga kwalejin horas da malamai ta Dogon-Daji a 1984. Daga nan kuma ya shiga jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto inda ya karanci aikin shari’a a 1991.

Ya kammala karatun koyon aikin shari’a na shekara daya a Legas a 1992.

Siyasa

Hakkin mallakar hoto
Aminu Tambuwal

Tambuwal ya fara koyon harkokin majalisa daga 1999 zuwa 2000 lokacin da yake aiki a matsayin mataimaki kan harkokin majalisa ga Sanata Abdullahi Wali, wanda a lokacin yake rike da mukamin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa.

A 2003, ya nemi kujerar wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal.

An zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai karkashin jam’iyyar ANPP.

‘Yan watanni gabanin zaben gwamna a 2007, Tambuwal ya koma PDP tare da tsohon gwamnan Sokoto.

Tambuwal ya rike mukamai a majalisar wakilai. A 2005, ya zama shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai har zuwa lokacin da ya koma PDP.

Bayan an sake zabarsa a 2007, an kuma sake zabarsa a matsayin mataimakin shugaban bulaliyar majalisar.

Tambuwal ya kuma rike shugabancin kwamitocin majalisar da dama ciki har da kwamitin dokoki da kasuwanci da na sadarwa da kuma na shari’a.

Ya kuma kasance mamba a kwamitin wucin gadi kan yi wa kundin tsarin mulkin kasa garambawul.

Tambuwal ya zama shugaban majalisar wakilai ta 10 cikin rudani

Hakkin mallakar hoto
Tambuwal’s Twitter

A watan Yunin 2011 ne Aminu Waziri Tambuwal ya zama shugaban majalisar wakilan Najeriya ta 10 a cikin wani yanayi mai sarkakiya kuma na ba-sabun-ba.

Tambuwal ya karbi rgamar majalisar ne daga hannun tsohon shugaban majalisar Dimeji Bankole.

Sakamakon rashin jituwa tsakanin majalisar ta wakilai da bangaren zartaswa, fadar gwamnati ta yi yunkurin ganin ta dasa shugabannnin majalisa da za su saurare ta.

To amma bisa rashin sa a sai aka samu ‘yan majalisar sun yi wa bangaren zartarwar kwanta-kwanta inda suka zabi mutumin da ba shi bangaren na zartarwar ke so ba.

A lokacin dai sai da ta kai ga jami’an tsaron ‘yan sanda sun kulle majalisar a ranar da aka sa ran zaben shugabannin majalisu, inda wasu da dama daga cikin ‘yan majalisar suka yi ta haurawa gini ta kan katanga.

Rahotanni na cewa shi kansa Aminu Tambuwal sai da ya yi shigar burtu sannan ya samu ya shige duk da cewa wasu rahotannin na cewa Tambuwal ya kwana a cikin ginin majalisar ne.

Rashin jituwar Tambuwal da Bangaren zartarwa

Ku san za a iya cewa rashin jituwa tsakanin bangaren majalisar wakilai da na zartarwa bai taba kamari ba kamar lokacin wa’adin shugabancin Aminu Waziri Tambuwal, tun bayan zangon mulkin Ghali Umar Na-Abba da shugaba Obasanjo.

Aminu Waziri Tambuwal ya kasance wani shugaban majalisa mai kwarjini da karfin fada a ji a tsakanin ‘yan majalisu.

Za a iya cewa Tambuwal bai samu wata cikakkiyar hamayya ba a cikin majalisa sabanin sauraran takwarorinsa shugabannin na majalisa.

La’akari da irin karfin fada a ji da Aminu Tambuwal yake da shi a majalisa ya sa bangaren gwamnati ya yi ta ‘kitsa’ tunbuke shi daga majalisa.

Aminu Tambuwal dan takarar shugaba kasa

Hakkin mallakar hoto
Tambuwal’s twitter

Tun dai kafin barin Aminu Waziri Tambuwal kujerar shugabancin majalisa a 2015, ya bar jam’iyyar PDP zuwa ta New PDP, kafin daga bisani ya bi Sanata Kwankwaso da Sanata Bukola da Gwamna Magatakarda Wamako da Atiku Abubakar zuwa jam’iyyar APC.

A shekarar ta 2015 ne Aminu Tambuwal ya zama gwamnan jihar Sokoto karkashin jam’iyyar ta APC.

A shekarar 2018 ne kuma gwamnan na Sokoto ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar ta APC, inda ya zo na biyu bayan Atiku Abubakar.

Daga nan kuma sai Aminu Tambuwal ya yi wa takarar gwamnan jihar ta Sokoto kome inda hukumar zabe ta ce shi ne ya lashe zaben bayan zuwa zagaye na biyu na kada kuri’a.

Kalubalen da ke gaban Tambuwal

Hakkin mallakar hoto
Tambuwal Twitter

Jim kadan bayan hawan Aminu Tambuwal kujerar gwamnan jihar Sokoto, sai ya fara samun rabuwar kai da tsohon gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko wanda shi ne ya mara masa baya lokacin takararsa.

Rashin jituwar ya tsamama sosai abin da har ya kai ga gwamna Tambuwal rushe majalisar zartarwa.

Mataimakin gwamna Tambuwal wanda shi ne abokin hamayyarsa a zaben 2019, Ahmed Aliyu ya yi murabus daga kujerarsa sakamakon girman barakar da ke tsakanin bangaren Tambuwal da na Magatakarda Wamakko.

Masu sharhi na ganin babban kalubalen da ke gaban Gwamna Tambuwal bai wuce na hada kan jama’ar jihar Sokoto ba da kansu ya dare sakamakon rashin jituwar gwamnan da ‘uban gidansa’.

Sauran kalubalen su ne wadanda suka yi wa jihar Sokoto dabaibayi kamar haka;

  • Ilimi
  • Ci gaba
  • Tsaro
  • Noma da kiwo

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...