Memphis Depay ya ci kwallo biyu ya bayar an zura daya a raga a wasa uku a Barcelona

Memphis Depay

Asalin hoton, Barcelona FC

Barcelona ta doke Getafe 2-1 a wasan mako na uku a gasar La Liga da suka fafata a Camp Nou ranar Lahadi.

Minti biyu da fara wasa Sergi Roberto ya ci wa Barcelona kwallo, sai dai minti 16 tsakani Getafe ta farke ta hannun Sandro Ramirez.

Sauran minti 15 su je hutu ne Memphis Depay ya ci wa Barcelona kwallo na biyu da ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.

Depay ya zama dan wasan Barcelona na biyu da ya ci kwallo ko ya haddasa aka zura a raga a wasa uku a kungiyar da fara kakar La Liga.

Cesc Fabregas shi ne ya fara yin wannan bajintar a kakar wasan La Liga ta 20111.

Depay shine ya bayar da kwallon da aka fara cin Real Sociedad a wasan makon farko a gasar La Liga ta shekarar nan.

Haka kuma shine ya ci wadda Barcelona ta tashi 1-1 a Athletic Bilbao a wasan mako na biyu, sannan ya ci Getafe a karawar mako na uku a kakar La Liga ta bana.

Depay ya koma Barcelona ranar 1 ga watan Yuli daga Lyon, bayan da kwantiragin sa ya kare a kakar da ta wuce.

Mahukuntan gasar La Liga sun dage karawar mako na hudu tsakanin Sevilla da Barcelona, domin bai wa kungiyar damar buga wasan farko a Champions League na bana.

Barcelona za ta karbi bakuncin Bayern Munich a karawar cikin rukuni a gasar Zakarun Turai ranar 14 ga watan Satumba.

Daga nan kuma Barcelona za ta yi wasa na mako na biyar a La Liga da Granada a Camp Nou ranar 19 ga watan Satumba.

(BBC Hausa)

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...