Me ya sa mutane masu son kansu ba su da kawaici?

Narcissism

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

(BBC Hausa)

Masu son kansu na da wani tunani na cewa suna da matukar muhimmanci sannan ba su da kawaici, amma masana halayyar dan Adam sun ce akwai yiwuwar cewa sun fi mafi yawan mutane farin ciki.

Wani bincike da ake gudanarwa kan masu son kai a Jami’ar Queens da ke Belfast ya gano cewa irin wadannan mutanen na da ban haushi amma da wuya wani abu ya dame su.

Masanin halayyar dan Adam Dakta Kostas Papageorgiou ya ce kushe halin son kai na iya rinjayar abubuwan kwarai ga masu son kai.

Masu binciken sun dade suna kokarin gane dalilin da ya sa ake ganin kamar masu son kai ke karuwa a al’umma- a siyasa da shafukan sada zumunta da taurarin fina-finan- da kuma idan ana ganin cewa “hali ne mai muni”.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Sun bayyana masu son kai a matsayin masu son “nuna halaye na ko-in-kula da ganin sun fi kowa da ji da kansu da rashin nuna tausayi ga sauran mutane sannan ba su da kawaici”.

Da wadannan munanan halaye, masu binciken sun so abin da ya sa ake saurin gane halin son kai.

Son kai na daya daga cikin munanan halaye da masana halayyar dan Adam suka gano, tare da halin rashin damuwa da mutane da son cutar da mutane don jin dadi.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Amma binciken Dakta Papageorgiou da mutane 700 duk manya ya nuna cewa duk da cewa halin son kai na da mummunan tasiri ga al’uma, akwai alamar cewa masu halin na mafana da shi.

Babu mamaki suna kuntata wa mutane- amma masu halin son kai basu damu ba kwata-kwata da yadda suka bata wa mutane rai.

Ba su cika damuwa ba kuma ba sa jin wahalhalun rayuwa- suna da ji da kai.

‘Suna matukar son iko’

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wannna ya biyo bayan ayyukan da tawagar Belfast ta yi a baya, wanda ke nuna cewa masu halin son kai na da yiwuwar samun ci gaba a wajen aikinsu da rayuwarsu gaba daya- saboda suna da jajircewar da ke taimaka masu wajen farfadowa daga wulakanci.

Haka kuma, Dakta Papageorgiou ya duba yadda rarrabuwar halin son kai ke iya haifar da tunani iri-iri.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Amma masu halin son kai wanda ake iya juyawa na ganin wasu mutanen a matsayin masu “mugunta”.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Bai kamata a kalli wadannan halayen a matsayin masu kyau ko marassa kyau ba amma a matsayin halin dan Adam da Allah ya halicce shi da su, wanda kuma za su iya zama masu amfani ko masu muni ga al’uma.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...