Me ya sa Buratai zai koma Borno?

Za a sayo wa sojojin Najeriya karin makamai domin yakar Boko Haram

Ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali, ya umarci Babban hafsan sojin kasa na kasar Janar Tukur Buratai da ya ci gaba da kasancewa a arewa maso gabas har sai yanayin tsaro ya inganta a yankin.

Wannan na daya daga cikin sabbin dabarun da kasar ta Najeriya ke dauka dangane da yakin da take yi da mayakan Boko Haram wadanda suka kara kaimi wajen kai hare-hare kan jami’an tsaron kasar.

Ba da dadewa ba ne aka samu rahotannin da suka ce kungiyar ta Boko Haram ta kai hari kan sansanonin soji da ke jihar Borno, abin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojoji masu yawa.

Gwamnatin kuma ta ce za ta inganta walwalar sojin kasar, musamman wadanda ke fagen fama.

A wata sanarwa da kanar Tukur Gusau, mai magana da yawun ministan tsaro na kasar ya fitar, ministan ya kuma umarci babban kwamanda mai lura da runduna ta 8 ta sojijn Najeriya da ya mayar da hedikwatar tasa zuwa birnin Gusau na jihar Zamfara daga Sakkwato mai makwabtaka.

Yankin Zamfara dai, wuri ne da ke fama da ayyukan masu fashin shanu, da kuma ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kudin fansa.

Abin da ya kai ga cewa gwamnatin jihar ta Zamfara ta sanar da dakatar da wasu masu rike da sarautar gargajiya a jihar, bisa zargin su da hada kai da ‘yan bindiga masu addabar yankin.

Sanarwar ta nemi hafsan hafsoshi da babban hafsan sojin kasa da su gudanar da sauye-sauye a rundunonin Delta Safe a yankin Naija Delta da operation lafiya dole a arewa maso gabas da kuma Sharan Daji a jihar Zamfara.

Kazalika, Kanar Gusau ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci a sayo kayan yaki da gaggawa domin tukarar ‘yan ta’addan na Boko Haram.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...