Me kuka sani game da gidan Sardauna Ahmadu Bello da ke Kaduna? | BBC Hausa

Gidan Arewa, shi ne asalin gidan Sardauna, kuma yanzu Cibiyar Bincike da Adana Tarihi na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Najeriya.

An kafa cibiyar ne bayan kisan gillar da aka yi wa Firimiyan Arewa na farko Sardauna, a juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1966.

BBC ta samu shiga wannan cibiya kuma har cikin É—akin Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello Firiminiyan Arewa.

Daga cikin abubuwan tarihi da BBC ta gani a Gidan Arewa akwai ‘inda aka samu gawar Sardauna, wanda yanzu aka killace domin nuna alama.

Mun samu damar shiga falon Sardauna inda muka ga kayan da ya yi amfani da su. Mun ga gadonsa da agogonsa da darduma da carbi da littafin addini.

More News

Yadda rikici a kan gishirin N20 ya yi sanadiyyar mutuwar wani mutum a Kano

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekaru 45, ya gamu da ajalinsa a hannun kanen matarsa, wani Magaji Salisu saboda gishirin N20. Dan marigayin,...

Sojoji Sun Kashe Mayaƙan IPOB 5

Dakarun rundunar sojan Najeriya da kuma ta rundunar sojan ruwan Najeriya a ranar Talata sun kashe mayaƙan ƙungiyar IPOB guda biyar a yayin musayar...

ĆŠan agajin Izala ya samu lambar yabo, kujerar hajji, kyautar mota bayan ya tsinci naira miliyan 100 ya mayar wa mai su

Salihu AbdulHadi Kankia, mamba ne na kungiyar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya samu yabo da tukuicin mayar da...

Musulmi a Zaria sun yi taron addu’o’i saboda mummunan halin matsi da Najeriya ke ciki

Musulmi a garin Zaria na jihar Kaduna, sun gudanar da addu'a ta musamman domin neman taimakon Allah kan halin da 'yan Najeriya ke ciki...