MDD: ‘Yan Venezuela miliyan hudu sun bar kasar’ | BBC Hausa

Venezuela
Image caption

Yawancin ‘yan Venezuela sun tsallaka kasashe makofta dan samun sauyin rayuwa

Hukumomin agaji na MDD sun ce mutane miliyan 4 ne suka tserewa kunci, da matsin tattalin arzikin da Venezuela ke ciki.

A wani sabon rahoto da MDD ta fitar ya nuna tun daga shekarar 2015 ‘yan kasar ke ficewa sannu a hankali, inda adadin su ya kai sama da miliyan biyu, a watanni bakwai da suka wuce kuma kusan miliyan daya ne suka bar kasar.

Kasashen da ke karbar bakuncin ‘yan ciranin na tsananin bukatar taimakon kasashen duniya dan kulawa da su.

Matsin tattalin arzikin da Venezuela ta samu kan ta a ciki ya kai halin da abubuwan amfanin yau da kullum kamar kayan abinci, da magunguna na neman gagarar jama’a.

A bangare guda kuma shugaba Nicolas Maduro ya sanar da bude iyakar kasar da Colombia ta jihar Tachira da ke yammaci, daman ya bude iyakar su da Brazil a watan da ya gabata.

Tun a watan Fabrairu Mr Maduro ya rufe iyakokin Venezuela da wasu kasashe dan hana Amurka da kawayenta shiga da kayan agaji.

Mummunan halin da kasar ta samu kan ta a ciki ya ta’azzara a farkon wannan shekarar, lokacin da rikicin siyasa tsakanin gwamnatin shugaba Nicolas Maduro da jagoran ‘yan adawa Juan Guaido ta kara zafi.

Kasashe da dama kamar Amurka da kawayenta suka mara masa baya kan ayyaka kan shi a matsayin shugaban riko, da hakan ya janyo zanga-zanga ba dare ba rana ta kokarin tsige Mista Muduro daga mukaminsa.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...