Mayaƙan ISWAP 73 sun miƙa wuya ga sojoji a jihar Borno

Mayakan kungiyar ISWAP su 73 tare da iyalinsu ne suka mika kansu ga sojojin shiya ta ɗaya na rundunar Operation Haɗin Kai dake Borno.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan al’amuran tsaro da suka shafi yankin tafkin Chadi, 42 daga cikin yan ta’addar tare da iyalinsu da suka haɗa da maza 4 mata 10 da kuma kananan yara 28 da suka fito daga ƙauyukan Bula Bello, Zaramari da kuma Garno sun miƙa kansu a ranar Laraba.

Sojojin bataliya ta 202 dake Bama su ne suka karbe su.

Bayanin na Zagazola ya cigaba da cewa maza biyu da mata 7 da kuma yara 9 daga ƙauyukan Ngauri, Siraja da kuma Nbellana sun miƙa kansu ga dakarun bataliya ta 152.

Zagazola ya kara da cewa mambobin ISWAP 9 da manyan mata biyu daga Ukuba sun miƙa kansu ga rundunar soja dake Gwoza.

Wasu majiyoyi dake rundunar sojan Najeriya ta ce ana cigaba da tantance tsofaffin ƴan ta’addar kafin a miƙa su ga hukumomin da su ka kamata.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...