Matsayin majalisar dattijai kan ƙirƙirar sabbin jihohi 20 a Najeriya

Majalisar dattawa

Asalin hoton, @NgrSenate

Majalisar dattawan Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ƴan majalisar sun bayar da shawarar ƙirkiro wasu sabbin jihohi 20.

Majalisar ta ce an yi wa kwamitin da ke nazarin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima gurguwar fahimta kan matakin.

Mai magana da yawun majalisar Ajibola Basiru ya ce majalisa ba ta da hurumin bayar da shawara ko kuma gabatar kuɗirin ƙirƙirar sabuwar jiha sai idan kudirin ya yi daidai da sashe na 8 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Ɗan majalisar mai wakilar Osun ta tsakiya ya ce sashe na 8 na kundin tsarin mulki ya bayyana sharuɗɗa ka’idoji na ƙirƙirar sabuwar jiha a Najeriya.

Ƙa’idoji da sharuɗɗan ƙirƙirar sabuwar jiha a cewarsa sun haɗa da jin ra’ayin jama’a kuma sai an samu amincewar kashi biyu bisa uku na al’ummar yankin da ake da’awar neman sabuwar jihar da kuma amincewar majalisun tarayya.

“Don haka majalisar dattawa ba ta hurumin amincewa da sabbin jihohi saɓanin yadda aka ruwaito,” in ji sanarwar da kakakin majalisar Sanata Ajibola Basiru ta bayyana.

Sanarwar ta ce maimakon za ta gabatar da buƙatar ga Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC wadda za ta tabbatar da bin sharuɗɗa da ka’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada.

Sannan kuma sai ya samu amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na ƴan majalisar wakilai da dattaji da suka fito daga yankin da ake neman ƙirƙirar wata sabuwar jiha.

An fara bin tsarin yankuna ne a Najeriya lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai daga turawan Birtaniya a 1960.

A lokacin ƴancin kai akwai yankuna uku – yankin arewa da yammaci da gabashi kuma an ci gaba da bin tsarin har 1960.

A 1987 – bayan shekara 27 aka samu jihohi 21 da kuma birnin Tarayya Abuja. An kuma sake ƙirƙirar wasu zamanin mulkin Janar Babangina

A 1996 zamanin Janar Sani Abacha jihohin Najeriya suka koma 36.

Masu neman sabuwar jiha na fafutika ne don cin gajiyar wasu albarkatu da kuma muƙaman gwamnati.

Wasu kuma masu sukar matakin na ganin za a ƙara wa Najeriya lodi musamman yanzu da ƙasar ke faɗi-tashi na biyan buƙatun johohi 36 haɗi da Abuja, kuma yanzu a ƙirƙiri wasu sabbi.

Suna kuma ganin wannan zai ƙara girman cin hanci da rashawa a Najeriya.

Asalin hoton, AFP

Sabbin jihohin da ake yaɗawa

Cikin rahotannin da ake yaɗawa, an fito da jerin sunayen sabbin jihohin da ake neman ƙirƙira daga wasu tsoffin Najeriya.

  • Jihar ITAI daga Akwa Ibom)
  • Jihar Katagum daga Bauchi
  • Jihar Okura daga Kogi ta gabas
  • Jihar Okun daga Kogi
  • Jihar Adada daga Enugu
  • Jihar Gurara daga Kudancin Kaduna
  • Jihar Ijebu daga Ogun
  • Jihar Ibadan daga Oyo
  • Jihar Tiga daga Kano
  • Jihar Ghari daga Kano
  • Jihar Amana daga Adamawa
  • Jihar Gongola daga Adamawa
  • Jihar Mambilla daga Taraba
  • Jihar Savannah daga Borno
  • Jihar Etiti daga kudu maso gabashin Najeriya
  • Jihar Orashi daga Imo da Anambra
  • Jihar Njaba daga Imo
  • Jihar Aba daga Abia
  • Jihar Anioma daga Delta
  • Jihar Torogbene da Oil River daga Bayelsa da Delta da jihar Rivers
  • Jihar Bayajida daga Katsina da Jigawa, da kuma Zamfara

More News

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Gidaje 8925

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara raba gidaje 8925  ga mutanen da suka nema kuma suka cancanci a basu a faɗin ƙasa baki ɗaya...

Ƴan Bindiga A Zamfara Sun Kashe Sakataren Jam’iyar PDP

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Musa Ille  sakataren jam'iyar PDP na ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara. Zagazola...