Matatar man Dangote ta sayo ɗanyen mai daga Brazil

Matatar Man Fetur ta Dangote ta  sayo ɗanyen man fetur daga ƙasar Brazil kamar yadda jaridar kasuwanci ta Bloomberg ta rawaito.

A ranar Juma’a jaridar ta wallafa cewa wannan ƙari ne kan yawan gangar ɗanyen manfetur ɗin da Najeriya ke shigowa da shi daga ƙasashen waje.

A cewar ƴan kasuwa dake da masaniyar cinikin, Matatar Dangote wacce har yanzu ke ƙoƙarin fara aiki ɗari bisa ɗari za ta karɓi gangar mai miliyan ɗaya nau’in Tupi daga Brazil da zai iso Najeriya a tsakiyar watan Agusta.

Ƴan kasuwar sun ce kamfanin man fetur na ƙasar Brazil,Petrobras shi ne ya sayar da man.

Jaridar Bloomberg ta ce jami’ai a kamfanin na Petrobras da kuma Dangote ba su ce komai kan batun bayan da jaridar ta tuntuɓesu.

More from this stream

Recomended