Matasan Arewa sun Allah-wadai da matakan hukumomin Lagos Da Rivers

A makon jiya ne gwamnatin Lagos ta kama tare da tsare wasu ‘yan jihar Jigawa su 121 da suka tafi ci rani Lagos, a dai-dai lokacin da al’ummar Musulmin Jihar Rivers, wadanda galibinsu ‘yan arewa ne, suka koka a kan matakin gwamnatin jihar na rusa masallacinsu na Juma’a a birnin Fatakol bisa ikirarin cewa, an gina shi ba bisa ka’ida ba.

Wannan lamari ya kai gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriyan ga shirya taron manema labarai a Kano domin kira ga hukumomin jihohin biyu su daina cin zarafin ‘yan arewa da ke zaune a jihohin nasu.

Shugaban gamayyar kungiyoyin ya bayyana rashin jin dadinsu ga yanda gwamnatin tarayya ta kama baki ta yi shuru a kan wannan batu, alhali ita ce keda hurumin ta shiga ta kwato wa duk dan kasa ‘yancinsa wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya basu cewa zasu iya zama a ko ina a cikin kasar.

Kungiyoyin matasan arewa sun yanke shawarar sa kafar wando daya da gwamnati wurin; an hana baiwa kamfanonin ‘yan kudu kwangila a arewacin kasar. Sun ce za su yi amfani da dokokin kasar wurin tabbatar da ganin an daina baiwa ‘yan kudu ayyukan kamar yanda su kuma suke hana ‘yan arewa a yankunansu.

Tuni dai shi ma tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana damuwa game da matakin, yana mai cewa, zai gabatar da batun a zauren Majalisar Dattawa kasar domin daukar mataki.

To amma a hira da wakilin sashin Hausa a Kano Mahmud Ibrahim Kwari, bayan taro da manema labarai a Kano, wakili a kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin na arewa, Alhaji Ashiru Shariff ya ce kungiyar ba za ta lamunta da matakin gwamntocin jihohin biyu ba.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...