Matakin rufe iyakar Najeriya da kasar Benin ya dakatar da harkokin kasuwanci

0

Rahotannin dake fitowa daga yankin iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin ta yankin garin Seme, na nuna cewa yanzu haka hukumomin tsaro a Najeriya sun rufe kan iyakar kasar da makwabciyarta.

Rufe kan iyakar dai ya haifar da rashin jin dadi ya kuma janyo hasarar ga ‘yan kasuwar dake kai da komo a duk rana domin saye da sayarwa.

Alhaji Faisal Ali Muhammed, shine Sarkin Hausawan garin Seme dake kan iyakar Najeriya da Benin, ya tabbatar da wannan lamari a wata hira ta wayar salula da wakilin muryar Amurka Babangida Jibrin ya yi da shi, yace bayan tarukan harkokin tsaro da suka gudanar da jami’an da aka turo daga Abuja, daga bisani an shaida masu cewar za’a rufe kan iyakar tsawon wata guda, domin tabbatar da tsaro, kuma duk da cewar lamarin ya haifar da matsaloli na kasuwanci, yana ganin da zarar an bude iyakar, komai zai daidaita.

Game da bayanin yadda matakin ka iya shafar tattalin arzikin kasashen biyu, Dr Dauda Mohammad Kontagora, ya ce akasarin kasuwancin da Najeriya ke yi da kasashe makwabtanta ana yin sa ne akan iyakar Najeriya da Jamhuriyar ta Benin, abinda kuma zai kawo cikas da koma baya.

Sai dai a cewar masanin yana ganin lamarin zai inganta kafin ma ya kai ga yin illa ga tattalin arzikin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here