Masu zuba jari ‘sun ja baya’ daga Najeriya | BBC Hausa

Wayar salula

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wayar salula na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Najeriya

Adadin jarin da ‘yan kasuwa na kasashen waje ke zubawa a Najeriya ya ragu da kashi 42 cikin dari, a cewar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya.

Masu zuba jarin sun ji takaicin yadda rikici ya barke tsakanin gwamnati da kamfanin MTN kan batun fitar da ribar da kamfanin ya samu daga kasar, kamar yadda rahoton Zuba Jari na duniya na majalisar ya bayyana.

“Jarin dala biliyan biyu kawai Najeriyar ta samu a bara”, duk da ikirarin da hukumomin kasar ke yi na cewa suna kyautata yanayin kasuwanci domin jan hankalin masu zuba jari.

Hakazalika bankunan HSBC da UBS sun rufe ofisoshinsu na Najeriya a shekarar 2018.

Koma-bayan da kasar ta samu ya zo ne duk da cewa nahiyar Afirka ta samu karuwar zuba jari daga kasashen ketare da kashi 13 cikin dari, abin da ya kawo karshen koma-bayan da aka shafe shekara biyu ana samu.

Rahoton ya kara da cewa ayyukan hakar sabbin ma’adinai da man fetur da kafa cibiyar kudi da kuma aiwatar da shirin cinikayya maras shinge tsakanin kasashen zai iya kara adadin jarin da ake zubawa a nahiyar.

Kasashen Kudancin Afirka su ne suka fi cin gajiyar wannan cigaban da aka samu, inda suka samu jarin dala biliyan 4.2 – kasar Afirka ta Kudu ce ke kan gaba sosai.

Gazawar da Najeriya ta yi ya bai wa Ghana, wacce ke kan ganiyar albarkatun mai da gas, damar zamowa sahun gaba a wuraren da ‘yan kasuwa suka fi son zuba jari.

Kasar Habasha ce kan gaba a yankin Gabashin Afirka, yayin da Kenya da Uganda da Tanzania ke biye mata baya.

More News

ÆŠalibai a Jami’ar Jos na zanga-zanga saboda rashin wuta da ruwa

Wasu daliban jami’ar Jos da ke jihar Filato a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matsalar karancin ruwa da rashin...

MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya. Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba...

Gwamnatin Kano Ta Rage ₦500,000 A Kuɗin Aikin Hajjin Bana

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar kyautar ₦500,000 domin su cika kuɗin...

Ƴan bindiga sun sace wani limami a jihar Kogi

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Quasim Musa babban limamin garin Iyara dake ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi. Lamarin ya faru ne a ranar...