Masu zanga-zanga sun lalata ofishin APC a jihar Ribas

Masu zanga-zangar matsin rayuwa  sun samu nasarar lalata ofishin jam’iyar APC a jihar Ribas.

Tun makon da ya wuce ne matasa dake faɗin ƙasarnan suka fantsama kan tituna inda suke zanga-zanga kan gwamnati ta kawo karshen matsin rayuwa da al’ummar Najeriya ke fuskanta.

Zanga-zangar ta haifar da lalata dukiyar gwamnati da ta al’umma a wurare daban-daban.

Da yakewa manema labarai jawabi a birnin Fatakwal ranar Talata shugaban riƙon jam’iyar APC a jihar ta Ribas, Tony Okocha ya ce ya yi mamakin dalilin da ya sa aka kai ofishin jam’iyar APC hari a jihar.

Okocha ya zargi gwamnatin jihar da da hannu dumu-dumu akai hari kan sakatariyar.

Ya ce suna da labari cewa ɗaukar nauyin mutanen da suka farma ofishin aka yi da kuma wanda ya ɗauki nauyinsu.

More from this stream

Recomended