Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin jakadancin Faransa a Jamhuriyar Nijar

Ofishin jakadancin Faransa a Jamhuriyar Nijar ya fuskanci hari daga wasu masu zanga-zanga dake goyon bayan juyin mulkin sa sojoji suka yi.

A ranar Laraba ne, Amadou Abdramane ya sanar da hambarar da gwamnatin shugaban kasa, Mohamed Bazoum.

A wani abu da ake gani kamar zanga-zanga ce kan zargin shirin tsoma bakin kasar Faransa kan sha’anin kasar Nijar magoya bayan jagoran mulkin sojan sun yi gangami a cikin garin Niamey inda suke daga tutar kasar Russia tare da kiran sunan, Vladimir Putin.

More from this stream

Recomended