Masari ya bayyana Dalilin da ya sa ya ce ‘yan Katsina su dauki makamai su kare kansu

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana dalilinsa na yin kira ga al’ummar jiharsa da su nemi makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a Katsina wanda aka yaÉ—a kai tsaye ta kafar Facebook, ya ce dole ne al’umma su tashi tsaye domin babu isassun jami’an tsaron da za su kare su.

Masari ya rika amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin wannan taro, kuma cikin tambayoyin da aka masa har da wadanda suka shafi harkokin tsaro.

Ya yi iƙirarin cewa an samu sauƙi a jihar Katsina duk da cewa abubuwa sun tsananta a Jihar Sokoto cikin kananan hukumomi guda biyu.

Gwamnan wanda a baya yake É—a’awar sulhu da Æ´an bindiga kafin ya yi watsi da manufar, ya ce ‘yan sandan da ke jiharsa ba su kai 3,000 ba, yana mai cewa gwamnati za ta taimaka wa masu son mallakar makaman don taimaka wa harkar tsaro.

“Harkar tsaron nan ta kowa da kowa ce babu bambancin siyasa – abin da mutane ya kamata su sani shi ne a Katsina ba ka da ‘yan sanda 3,000…saboda haka muke kira ga duk wanda zai iya ya nemi makami ya kare kan sa da iyalansa,” in ji Gwamna Masari.

Ya ci gaba da cewa: “Shari’ar Musulunci ma ta yarda mutum ya kare kan sa da dukiyarsa da iyalansa. Idan ka mutu kana Æ™oÆ™arin kare kanka ka yi shahada. Abin baÆ™in ciki ma shi ne ta yaya ‘yan fashi za su samu bindiga amma mutanen kirki ba su da ita da za su kare kansu da iyalansu.”

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa za ta taimaki duk wanda yake son ya mallaki makami don daÆ™ile ayyukan ‘yan fashi. “Za mu taimaki waÉ—anda ke son shigo da makamai saboda akwai buÆ™atar ‘yan Katsina su taimaka wa jami’an tsaro.”

Masari ya ce idan ka zuba sojojin Najeriya gaba daya a dajin Zamfara za su bace ne domin yawansu ba zai iya game dajin ba baki daya, don haka dole a hada karfi da karfe a kare kai baki daya.

Sai dai gwamnan ya soki ayyukan ‘yan sa-kai (‘yan banga), yana mai cewa “ba mu yarda da aikin ‘yan sa-kai ba saboda Æ™aura suke yi daga garinsu zuwa wani gari, mun fi son mutane su kare garuruwansu da kansu”.

Ya ce akwai bukatar komawa baya a fahimci menene ya fara jawo wannan matsalar ta tsaro da haka ne kawai za a iya lalubo bakin wannan matsala da ta gagarin kwandila.

Ya yi suka ga masu zanga-zanga musamman wadanda suke hawa titina su rufe hanya, su hana al’umma harkokinsu na yau da gobe.

Inda ya kalubalanci wadanda ke hakan da indai mazaje ne su, “lokacin da aka yi kuruwa su fito domin kare jiharsu da iyalansu”.

Masana harkar tsaro irin su Manjo Lawal Galma mai ritaya, wani masanin tsaro a Najeriya na ganin hakan gazawa ce.

A hirarsa da BBC Hausa ya ce, “duk lokacin da ka ji manya na kiraye-kirayen cewa mutane su É—auki makamai su kare kansu to gazawa ce.

“Idan ka ce a É—auki makamai to waÉ—anne irin makamaki kake nufi. Dole idan za ka kare kanka dole makaminka ya fi na masu kawo maka hari Æ™arfi.”

Ya ce sauƙin abin ma idan gwamnatin ce za ta samar da makaman. Kamar misali bai wa ƴan sa kai taimako na irin makaman da za su fatattaki maharan.

A ganinsa bai wa kowa dama ya mallaki makami tamkar ba da damar bazuwar makamai ne ba bisa Æ™a’ida ba.

“Gaskiya ya dai kamata gwamnati ta fara tunanin wata hanyar ta daban amma ba ta bai wa mutane damar É—aukar makamai ba,” ya Æ™ara da cewa.

Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya na fuskantar matsalar ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane kamar jihohin Zamfara da Kebbi da Sokoto da kuma Kaduna.

An yi garkuwa da daruruwan mutane a Katsina a wannan shekarar yayin da dubban mutane suka tsere suka bar muhallansu.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...