Masana kimiyya sun sako sauraye cikin jama’a | BBC Hausa

Mosquito

Hakkin mallakar hoto
Science Photo Library

Sakin saurayen da aka jirkita kwayoyin halittun nasu cikin jama’a, wani bangare ne na gangamin yaki da cutar maleriya baya-bayan nan a nahiyar Afirka.

Cutar zazzabin cizon sauro ta kashe fiye da mutum 4000 bara a Burkina Faso kuma ta kama fiye da mutum 12, 000

Yayin da masu sukar shirin ke bayyana damuwa, masana kimiyyan da ke cikinsa sun ce sakin saurayen wanda shi ne irinsa na farko a Afirka, manuniya ce ta wani muhimmin ci gaba a yakin da ake yi da sauro mai yada zazzabi.

Cibiyar binciken kimiyyar lafiya ta Burkina Faso ta saki saurayen da aka jirkita kwayoyin halittunsu cikin garin Bana wanda ke kudu maso yammacin kasar.

Matakin wani bangare ne na shirin gidauniyar Target Malaria mai bincike a kan harkokin lafiya karkashin jagorancin Jami’ar Bincike ta Imperial College da ke birnin London.

Ko da yake, sakin saurayen ya samu amincewar hukumar kare al’umma daga halittu ko sinadarai masu cutarwa ta Burkina Faso, amma masu sukar shirin sun bayyana damuwa game da hatsarin da ke tattare.

Inda suka tuhumi sahihancin shirin, da suka ce ba sa tsammanin yana da wani alfanu wajen takaita yaduwar cutar zazzabin cizon sauro.

Gidauniyar Target Malaria ta ce ba a saki mazajen saurayen da nufin rage bazuwar cutar maleriya ba amma matakin zai taimaka wa kwararru wajen tattara muhimman alkaluman da za su tallafi bincikensu.

Cibiyar Binciken ta Burkina Faso ta ce an saki saurayen ne bayan an yi la’akari da duk wasu sharuddan ya kamata da tsare-tsaren hukuma, haka zalika al’ummomin yankin su ma sun amince da wannan shirin bayan tuntubarsu da aka yi.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...