Maryam Yahaya: Tauraruwar fina-finan Kannywood ta ce maleriya da taifod ne ke damunta

Instagram//real_maryamyahaya

Asalin hoton, Instagram/

Tauraruwar fina-finan Kannywood Maryam Yahaya ta bayyana cewa tana fama da cutar maleriya da taifod, shi ya sa aka ji ta shiru ba ta fitowa a fina-finai.

Ta bayyana haka ne a wata hira da BBC domin yin watsi da rahotannin da ke cewa tana fama da cutar da ta danganci jifan aljanu.

Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, wanda ya yi tafiyayya zuwa gidan su tauraruwar, ya ce ta yi matukar ramewa.

Sai dai a cewarta: “Na yi taifod da maleriya ne, ina kan yi. Amma yanzu jiki Alhamdulillahi, na samu lafiya.”

Da take amsa tambaya kan raÉ—e-raÉ—in da ke cewa an yi mata asiri ko jifa, tauraruwar ta ce “gaskiya ni ba jifa ba ne ya dame ni don ban ma san shi ba.”

Ta ce ta kwashe fiye da wata É—aya tana fama da rashin lafiya, tana mai cewa yanzu tana samun sauki sosai, “sai dai rashin Æ™wari kuma dama sai a hankali Æ™wari yake zuwa.”

A nasa bangare, mahaifin tauraruwar, Alhaji Yahaya Yusuf, ya ce ‘yar tasa ta kwana biyu a kwance kuma sun kai ta asibiti.

Ya kara da cewa yanzu suna haÉ—a maganin asibiti da na Hausa, inda ya sa malaman addini suke yi mata addu’a.

Ya ce tabbas maleriya da taifod ne ke damun ‘yarsa yana mai yin watsi da masu yaÉ—a jita-jitar cewa an jefi ‘yar tasa.

Matashiyar tauraruwar mai shekara 20 ta fara haskawa ne a cikin fim dinta na farko mai suna Mansoor.

More News

An kori sojojin Najeriya biyu saboda satar kebul a matatar Dangote

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da korar wasu sojoji biyu da ake zargi da satar igiyoyin sulke a harabar matatar Dangote da ke jihar...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

Sojoji sun gano masana’antar Æ™era bom a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun gano wata masana'anta da mayaƙan kungiyar ISWAP suke ƙera bama-bamai. Masana'antar ƙera bama-bamai an gano ta ne a Abulam-BUK dake...

Atiku ya ziyarci Abdul Ningi

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci dakataccen ɗan majalisar dattawa sanata, Abdul Ningi dake wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa. Atiku...